Da duminsa: Hotunan NLC yayin da suka fito zanga-zangar kara ga ASUU

Da duminsa: Hotunan NLC yayin da suka fito zanga-zangar kara ga ASUU

  • Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, ta fito zanga-zanga a wasu jihohin kasar nan domin taya ASUU fushi
  • Kamar yadda hotuna suka bayyana, mambobin NLC sun fito zanga-zangar a titunan Legas da Kano a Najeriya
  • Tun dai a watan Fabrairu ne ASUU ta fada yajin aiki wanda har yanzu babu batun sasanci tsakaninta da gwamnatin tarayya

A yau ranar Talata, 26 ga watan Yulin 2022 ne Kungiyar Kwadago ta kasa ta bayyana a titunan jihohin kasar nan domin zanga-zangar kara ga Kungiyar Malamai masu koyarwa na jami'o'in Najeriya.

Idan za a tuna, Kungiyar Malaman sun shiga yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 kuma har yanzu babu batun sasanci tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

NLC Protest
Da duminsa: Hotunan NLC yayin da suka fito zanga-zangar kara ga ASUU. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Sakamakon halin ko in kula da gwamnatin tarayya ta nuna wa ASUU, ya tunzura kungiyoyi masu yawa ciki kuwa har da kungiyar Kwadago ta kasa wacce ta fito taya su nuna fushi a titunan jihohin kasar nan.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ma'aikatan wutar lantarki za su mamaye Najeriya domin taya ASUU zanga-zangar nuna fushi

Ga wasu daga cikin hotunan 'yan kungiyar kwadagon daga jihohin Legas da Kano a Najeriya:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NLC Kano
Hotuna: NLC ta fito zanga-zangar kara ga ASUU a jihohin Najeriya. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

NLc Kano
Hotuna: NLC ta fito zanga-zangar kara ga ASUU a jihohin Najeriya. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

NLC Kano
Hotuna: NLC ta fito zanga-zangar kara ga ASUU a jihohin Najeriya. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

NLC Kano
Hotuna: NLC ta fito zanga-zangar kara ga ASUU a jihohin Najeriya. Hoto daga The Cable
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng