Gwamnan Jihar Imo Ya biya Masu Sayar da Albasa Da Shanu Diyyar Milyan 30

Gwamnan Jihar Imo Ya biya Masu Sayar da Albasa Da Shanu Diyyar Milyan 30

  • Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma, ya ba wa yan kasuwar albasa da masu sayar da shanu diyyar Naira miliyan N30 bayan asarar da suka tafka a bara
  • Shugaban Kungiyar manoma da sarrafa albasa ya ce asarar da suka yi ya wuce diyyar da aka biya su
  • Halilu Muhammad, ya ce Matsalolin da suka shiga ta hanyar harin yan bindiga a jihar Imo ba zai hana su cigaba da kasuwancin su a yanki kudu ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya bayar da gudummawar zunzurutun kudi har naira miliyan 30 ga ‘yan kungiyar Albasar masu sarrafa kayayyaki da masu sana’ar sayar da dabbobi da kuma masu sayar da shanu da suka yi asarar kayayyakinsu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a jihar Imo a bara.

Yan kasuwan sun tafka asarar ne lokacin da wasu gurbatattun mutane suka kai masu hari a kasuwar sayar da albasa da ke Ƙaramar Hukumar Ahiazu Mbaise da ke Jihar Imo.

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya raba tsabar kuɗi miliyan N172m da abinci ga talakawa 30,436 a karamar hukuma ɗaya

Kungiyar manoman albasa ta Najeriya ta tabbatar da cewa Gwamnan ya ba wasu daga cikin yan kungiyar naira miliyan goma sannan yaba masu sayar da shanu da al’amarin ya shafa naira miliyan 20 a matsayin diyya.

Arewa
Gwamnan Jihar Imo Ya biya Masu Sayar da Albasa Da Shanu Diyyar Hoto Milyan 30 Legit.NG
Asali: Getty Images

Shugaban kungiyar noma da sarrafa albasa reshen jihar Imo Halilu Muhammed, da yake zantawa da wakilan BBC yace asarar da yan kasuwan suka yi ya wuce Naira miliyan N13 amma gwamnan Hope Uzodimma ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba a yin ɓari a kwashe duka.

Halilu Muhammad ya ce, shugaban ƙungiyar manoma albasa ta Najeriya baki ɗaya Aliyu Maitasamu Isa ya rabawa waɗanda lamarin ya shafa kason su.

Gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma, ya musu alkwarin cewa irin haka ba zai sake faruwa ba, kuma tun bayan iftila'in da ya faru da su, gwamnan ya ƙara tsaurara matakan tsaro a wuraren da yan yankin Arewa ke sana'ar su.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Halilu Muhammad, ya kara da cewa duk da matsalolin da suka fuskanta ta sanadiyyar hare-haren ƴan bindiga, ƙungiyar tasu za ta ci gaba da sana’ar ta a kudancin kasar.

An Gurfanar Da wani Likitan Birtaniya Da Laifin Hada Baki Da Ekweremadu Kan Girbin Koda

A wani labari Kuma, Wani Likitan da ke birnin Landan ya hada kai da Sanata Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice, a Burtaniya da shirin girban kodar wani dan Najeriya mara galihu.

Obinna Obeta, mai shekaru 50, dake zama a Landan, ya bayyana a kotun Majistare ta Bexley a ranar 13 ga watan Yuli, bisa zargin hada baki da Ekweremadus don shirya tafiyar Ukpo Nwamini David mai shekaru 21 daga Najeriya zuwa Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa