Kowa yana amfana da rashin tsaro, hatta gwamnati: Ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga yayi fallasa

Kowa yana amfana da rashin tsaro, hatta gwamnati: Ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga yayi fallasa

  • Kasurgumin shugaban 'yan bindiga a jihar Zamfara, Abu Sanni, yace rashin tsaro yanzu kasuwanci ne dake ci sosai
  • Ya fallasa cewa, gwamnati tana samun kudi daga farmakin da suke kaiwa, su ma kuma suna samu amma dole sai sun zubar da jini
  • Ya sanar da yadda suka sace 'yan matan makarantar Jangebe don fusata gwamnati kuma suka karbe N60 miliyan na kudin fansa

Zamfara - Abu Sanni, daya daga cikin gagaruman shugabannin 'yan bindiga a jihar Zamfara, yace rashin tsaro yanzu ya zama kasuwancin da kowa ke amfana da shi.

Sanni, wanda yace ya taimaka wurin sace 'yan matan makarantar sakandare ta gwamnati dake Jangebe a Zamfara, ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi da BBC Africa Eye a dajin Zamfara.

'Yan bindiga
Kowa yana amfana da rashin tsaro, hatta gwamnati: Ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga yayi fallasa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ma'aikatar ilimi ta ba da umarnin garkame makarantun gwamnatin tarayya na Abuja

Yusuf Anka, wani 'dan jarida wanda ya zaga maboyar 'yan bindigan dake jihar ya samu tattaunawa da su.

Sanni ya sanar da manema labarai cewa, sun sace 'yan matan a ranar 27 ga watan Fabrairun 2021 kuma kungiyarsa ce ta aiwatar domin daukan fansa kan yadda gwamnati ta aiko sojoji suka yi musu luguden wuta.

Yace kungiyarsa ta bukaci N300 miliyan daga gwamnati domin su saki 'yan matan amma N60 miliyan kacal aka biya su.

"Bayan damina ta kare, sai suka turo sojoji wurinmu. Mun yanke shawarar nunawa gwamnati cewa ta daina shiga cikin matsalarmu. Mun je Jangebe kuma muka sace dalibai. Muna son fusata gwamnati ne," yace.
"Mun bukaci kudin fansa har N300 miliyan, bayan sasanci mun samu N60 miliyan."

Sanni yace rashin tsaro yanzu kasuwanci ne mai ci sosai inda ya kara da cewa kowa hatta gwamnati tana amfana daga miyagun farmakin da suke kai wa.

Yace: "Saboda ya riga ya zama kasuwanci. Hakan ne yasa abubuwa ke cigaba da tabarbarewa tun daga sama har kasa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

"An ce idan akwai rashin tsaro, gwamnati na samun kudi. Kowa yana amfana. Mu ma muna samun kudi. Duk da mu kudinmu sai an zubar da jini sannan ya cigaba da shigowa."

Mansurah ga Tinubu: Zan yi maka kamfen da jinina, kyauta, in ka ceto fasinjojin jirgin kasan Abj-Kd

A wani labari na daban, bayyanar bidiyon fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda ke hannun masu garkuwa da mutane ya tada hankulan 'yan Najeriya.

A sabon bidiyon da suka saki, an ga yadda suke zane jama'ar da ke hannunsu da sanyin safiya inda fasinjojin ke ta kuka cike da ban tausayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng