Jikokin Gwamna El-Rufai sun tsallake rijiya da baya, an gano sabuwar mai rainonsu na dauke da cuta
- Sirikar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Halima Nwakaego, ta bayyana yadda suka dauka sabuwar mai rainon yara amma tana dauke da cuta
- Ta shawarci iyaye mata su dage wurin yi wa hadiman cikin gida ballantana masu raino gwajin kanjamau, TB, Hepatitis da sauransu
- Ta yi bayanin cewa, bayan gano mai rainon na dauke da cuta, daga bisani ta bayyana cewa shekarunta 7 da cutar amma ta boye musu
Kaduna - Matar 'dan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Halima Kazaure Rufai, ta bayyana yadda tagwayenta suka tsallake rijiya da baya.
Matar 'dan takarar majalisar wakilan a jihar Kaduna, Bashir Ahmad El-Rufai, ta sanar da yadda suka gano sabuwar mai rainon 'ya'yansu na dauke da cuta.
Lamar yadda LIB ta ruwaito, sirikar gwamnan, Halima Nwakaego, ta shawarci jama'a, ballantana iyaye mata da su dinga yi wa hadiman cikin gida gwanin Kanjamau, TB, Hepatitis da sauran cutuka kafin su dauke su aiki.
Mahaifiyar tagwaye duka maza, kuma matar Bashir El-Rufai, ta bada wannan shawarar ne ta Instagram a ranar Lahadi, 24 ga watan Yulin 2022 bayan mai rainon yara da ta dauka ta tabbata dauke da cuta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda Halima tace, mai rainon da farko ta nuna bata san tana dauke da cutar ba amma daga bisani ta tabbatar da cewa ta kwashe tsawon shekaru bakwai tana dauke da cutar.
A wallafarta:
"Barkanmu da safiya iyaye mata. Don Allah a dinga yi wa masu raino gwaji da sauran ma'aikata. Ballantana idan akwai yara.
"Ku yi musu gwajin Kanjamau, TB, Hepatitis da sauransu. A cikin kwanakin nan ne muka samu mai raino wacce ta san tana dauke da daya daga cikin wadannan cutukan amma ta ki fada mana.
"Mun yi mata gwaji, aka tabbatar tana dauke da cutar kuma sai take nuna kamar bata san tana da ita ba. Bayan takura mata kan lamarin, daga bisani ta amsa tana da cutar tun shekaru bakwai da suka wuce. Ba wannan bace mai raino ta farko da muka taba samu haka. Don Allah a dinga yin gwaje-gwaje kafin daukarsu aiki. Mu zama lafiya."
Hotuna: Ango ya zabi doki matsayin babban abokinsa a aurensa, har amarci ya tafi da shi
A wani labari na daban, wani masoyin doki ya yanke hukuncin amfani da ingarman dokin da yafi kauna a matsayin babban abokinsa a ranar aurensa kuma har ya kai ga tafiya da shi cin amarci.
Paul Boyles mai shekaru 47 ya shirya yadda dokinsa ya taya shi karbar aure a ranar aurensa sa masoyiyarsa Kay mai shekaru 48.
Asali: Legit.ng