Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Mai Shari'a Monica, Ta Yi Rashin Wani Ɗanta
- A karo na biyu, ɗan shugabar Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya, Mai shari'a Monica, ya rasu daga kwanciya bacci ranar Asabar
- Bayanai sun tabbatar da cewa marigayin wanda ya karanci lissafi, yana aiki ne da ma'aikatar sufuri ta ƙasa a jihar Legas kamin rasuwarsa
- A shekarar 2011, Mai shari'a ta rasa babban ɗanta na fari, wanda ya rasu bayan wani direban daki ka tsere ya kaɗe shi a Jos, jahar Filato
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugabar Kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, Mai shari'a Monica Dongban-Mensem, ta ƙara yin wani babban rashi na ɗanta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ɗan da ta haifa na biyu, Prince Paeke Shapnaan Dongban, ɗan kimanin shekara 38 a duniya ya rasu yana cikin bacci da safiyar ranar Asabar.
Wata majiya ta tabbatar da rasuwar ga manema labarai da cewa tuni iyalan gidan Alkalin suka shiga cikin duhu da jimamin wannan rashi.
Marigayin, wanda ya karanci darasin Lissafi (BSc Mathematics) a jami'ar fasaha ta tarayya da ke Minna, jihar Neja, ya na aiki ne a ma'aikatar Sufuri ta ƙasa a jihar Legas lokacin rayuwarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda Mai Shari'an ta rasa ɗanta na fari
Wannan rasuwa na zuwa ne shekaru 11 bayan mutuwar ɗan shugabar Kotun na fari watau Kwapda’as Rangna’an Samson Dongban.
Ɗanta na farko ya mutu ne bayan wani direban daki ka tsere ya kaɗe shi a Jos, babban birnin jihar Filato, a shekarar 2011, the nation ta ruwaito.
Sai dai bayan rasuwarsa, Mai Sharia Monica, ta kafa gidauniyar kare haɗurra, 'Kwapda’as Road Safety Demand Foundation' domin tuna wa da babban ɗan ta.
A wani labarin na daban kuma kun ji cewa 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Babban Malami a mahaifar gwamnan Sakkwato
Kwanaki kaɗan bayan ɓinne Malamin Majami'ar Katolika, wanda aka sace kuma aka kashe shi a jihar Kaduna, yan bindiga sun sake garkuwa da wani a Sakkwato.
Wasu miyagun yan bindiga da ba'a gane ko su waye ba sun yi garkuwa da Malamin Coci, Tony Udemezue, wanda ke ƙarƙashin Cocin Ƙatolika na jihar Sakkwato.
Asali: Legit.ng