Dukan Fasinjoji: Iyalan Waɗan Da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Kewaye Ma'aikatar Sufuri

Dukan Fasinjoji: Iyalan Waɗan Da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Kewaye Ma'aikatar Sufuri

  • Iyalan fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da suka rage hannun yan bindiga sun mamaye ma'aikatar Sufuri ta ƙasa, Abuja
  • Hakan na zuwa ne awanni 24 bayan yan ta'adda sun fitar da bidiyon yadda suke azabtar da mutanen da duka
  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce ya sha nanata wa hukumomin tsaro su kubutar da mutanen

Abuja - Fusatattun iyalan Fasinjojin da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa sun kewaye hedkwatar ma'aikatar sufuri ta tarayya, sun hana ma'aiakta shiga ofisoshin su.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan zanga-zangar na zuwa ne awanni 24 bayan wani bidiyo da ya bayyana ya nuna yan ta'addan na dukan fasinjojin da suka rage a hannun su.

Iyalan fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna.
Dukan Fasinjoji: Iyalan Waɗan Da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Kewaye Ma'aikatar Sufuri Hoto: Punchng
Asali: Twitter

Yan bindiga sun yi garkuwa da Fasinjojin ne yayin da suka farmaki jirgin ƙasa da ke jigila tsakanin Kaduna-Abuja ranar 28 ga watan Maris, 2022, inda wasu mutum Tara suka rasa rayuwarsu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Bindige Sufetan Yan Sanda Har Lahira Yayin Harin Da Suka Kai Caji Ofis

Domin nuna fushin su kan abun da ke faruwa da yan uwansu, iyalan fasinjojin da safiyar Litinin suka mamaye ma'aikatar sufuri, da hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu zanga-zangar, waɗan da ke ɗauke da Alluna, sun bukaci gwamnati ta kuɓutar musu da yan uwan su, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Har yanzun da muka tattara wannan rahoton, ma'aikatan da ke aiki a ma'aikatar sufuri ba su samu hanyar shiga Ofisoshin su ba.

Zanga-Zanga a Abuja.
Dukan Fasinjoji: Iyalan Waɗan Da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Kewaye Ma'aikatar Sufuri Hoto: @punchng
Asali: Twitter

Wane mataki FG ta ɗauka?

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari. ya sake nanata cewa tuni ya ba hukumomin tsaro umarnin su kuɓutar da fasinjojin.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun bayan harin kwana 122 kenan wanda yan ta'adda suka sace Fasinjoji sama da 60, aƙalla 20 sun kuɓuta bayan biyan fansar miliyan N100m kowane ɗaya, har yanzu sama da 40 na hannun su.

Kara karanta wannan

Dukan Fasinjojin Jirgin Kasa: Duk Munafukai Ne Masu Allah Wadai A Soshiyal Midiya, Naziru Sarkin Waka

Wata majiya ta faɗa wa jaridar cewa yan bindigan sun ɗauki matakin dukan fasinjojin ne domin nuna fushin su kan hana biyan fansar wasu daga cikin mutanen.

Zanga-zanga a Abuja.
Dukan Fasinjoji: Iyalan Waɗan Da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Kewaye Ma'aikatar Sufuri Hoto: @punchng
Asali: Twitter

Ɗaya daga cikin fasinjojin da suka yi magana a Bidiyon, Mukhtar Shu'aibu. ya tabbatar da cewa yan ta'addan sun fusata da hana biyan kuɗin fansan.

"Bamu san laifin da muka yi wa gwamnatin ƙasar nan ba, an haife mu a ƙasar nan, kwana 120 muna nan amma har yanzu gwamnati ta gaza ceto mu, laifin me muka yi?"
"Wasu daga cikin mu sun kusa kubuta a baya-bayan nan amma jami'an tsaro suka hana kuma suka dakatar da yan uwanmu zuwa wurin mu."
Zanga-zanga a Abuja.
Dukan Fasinjoji: Iyalan Waɗan Da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Kewaye Ma'aikatar Sufuri Hoto: @punchng
Asali: Twitter

A wani labarin kuma kun ji cewa a jiya wasu iyalan fasinjojin sun gudanar da zanga-zanga a Kaduna bayan fitar bidiyon duka

Wakilin mu ya ziyarci wurin kuma masu zanga-zangar sun shaida masa suna nuna fushin su ga halin ko in kula da FG ta nuna.

Kara karanta wannan

Biyan Kudin Fansa ya Jawo aka Lakadawa Fasinjojin Jirgin Kaduna-Abuja Mugun Duka

Zanga zangar a cewar Aisha MS Utaz, sun yi ta ne domin nuna bacin ransu akan yadda gwamnati ta yi kunnen uwar shegu akan bukatar da yan bindigar suka nema kafin sakin fasinjojin, ba tare da kuma Gwamnatin ta samar da wata maslahar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262