'Yan Sanda Sun Yi Ram Da Wasu Sojojin Bogi Guda Huɗu a Jihar Legas

'Yan Sanda Sun Yi Ram Da Wasu Sojojin Bogi Guda Huɗu a Jihar Legas

  • Dakarun hukumar yan sanda sun yi ram da wasu mutum huɗu sojojin bogi a jihar Legas da tsakar daren jiya
  • Mutanen hudu, maza uku da mace ɗaya, bayanai sun nuna cewa ɗayan su ya taɓa aiki da hukumar sojin Najeriya amma ta sallame shi a 2019
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an kai su sashin binciken manyan laifuka don tsananta bincike

Lagos - Jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Legas sun kama wasu mutum huɗu bisa zargin suna yi wa rundunar sojojin Najeriya sojan Gona a jihar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mutanen da suka shiga komar yan sandan kuma ake zargin su da yin sojan gona sun haɗa da maza guda uku da kuma mace ɗaya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: 'Yan bindiga sun kai kazamin hari kan matafiya a Katsina, sun kashe rayuka

Sojojin ƙara a jihar Legas.
'Yan Sanda Sun Yi Ram Da Wasu Sojojin Bogi Guda Huɗu a Jihar Legas Hoto: thenationonlineng.com
Asali: UGC

Dakarun yan sanda na Caji Ofis ɗin Iju sun samu nasarar kama mutanen ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren jiya Lahadi wayewar garin yau Litinin.

Haka zalika, bayanai sun nuna cewa an kama waɗan da ake zargin sanye da kayan Sojoji kuma a cikin wata motar Mazda3 saloon sun nufi wani wuri da ba'a sani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa ɗaya daga cikin mutanen da aka kama, wanda ake zargin shi ya samar musu da kayan sojojin, ya yi ikirarin cewa shi soja ne a baya amma hukumar soji ta kore shi a shekarar 2019.

Wane mataki hukumar yan sanda ta ɗauka?

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kame sojojin bogin ga manema labarai.

Ya ƙara da cewa a halin yanzun an kai waɗan da ake zargin sashin binciken manyan laifuka na jiha, (SCID), da ke Yaba domin cigaba da bincike kan su.

Kara karanta wannan

An kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga yana ɗaukar ma'aikata zasu sace jiga-jigan siyasa biyu a jihar Arewa

A wani labarin kuma Gwamnan Imo ya ce ba zai yi ƙasa a guiwa ba har sai zaman lafiya ya samu gindin zama a yankin su

Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya ce zai tabbatar da sun haɗa karfi da karfe wajen ganin zaman lafiya ya dawo a kudu maso gabas.

A wurin taron masu ruwa da tsaki na APC a yankin, gwamnan ya lashi takobin dawo da zaman lafiya kafin babban zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262