Ba zamu yi ƙasa a guiwa ba har sai zaman lafiya ya samu gindin zama a yankin mu, Uzodinma

Ba zamu yi ƙasa a guiwa ba har sai zaman lafiya ya samu gindin zama a yankin mu, Uzodinma

  • Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya ce zai tabbatar da sun haɗa karfi da karfe wajen ganin zaman lafiya ya dawo a kudu maso gabas
  • A wurin taron masu ruwa da tsaki na APC a yankin, gwamnan ya lashi takobin dawo da zaman lafiya kafin babban zaɓe
  • Mataimakin shugaban APC na shiyyar ya ce jam'iyyar ta yi abun a zo a gani don haka zata samu nasara a zabe na gaba

Imo - Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce gwamnatinsa zata tabbatar an haɗa ƙarfi da karfe wajen tabbatar da zaman lafiya ya dawo a kudu maso gabashin Najeriya kafin zaɓen 2023.

Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin taron masu ruwa da tsakin na APC reshen kudu maso gabas wanda ya gudana a Owerri, babban birnin jihar Imo ranar Asabar, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Ba zamu yi ƙasa a guiwa ba har sai zaman lafiya ya samu gindin zama a yankin mu, Uzodinma Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A wurin taron, gwamna Uzodinma ya soki yan siyasan da ke tsagin hamayya kuma ya zarge su da ƙin fitowa su yi Allah-wadai da kashe-kashe, lalata kadarorin gwamnati da ke faruwa a yankin.

"Ba abinda zai dakatar da mu wajen tabbatar da zaman lafiya ya dawo ya samu gindin zama a kudu maso gabashin Najeriya kafin zaɓen 2023."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wajibi mu matsa gaba, ranar da zan saki jihar nan ga yan ta'adda ba zata taɓa zuwa ba."

- Gwamna Uzodinma.

Da yake jawabi kan zaɓen 2023, Gwamna Uzodinma ya ce jam'iyyar APC ke jagorancin jihohi 22 kuma yana da kwarin guiwar cewa jam'iyyarsu zata samu nasara a wadan nan jihohin.

APC ta yi abin a zo a gani

An nashi jawabin mataimakin shugaban APC na shiyyar kudu maso gabas, Ijeoma Arodiogbu, ya ce jam'iyya mai mulki ta yi abun a zo a gani musamman a yankin tare da kammala aikin gadar Neja ta biyu.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

"Kan mu a haɗe yake zamu tabbatar ɗan takarar mu na shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu goyon bayan da ya dace shekara mai zuwa."

"Haka nan mun gamsu da zaɓinsa na ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa watau Sanata Kashim Shettima."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Kashe Wasu Sun Sace Da Yawa a Katsina

Tsagerun yan bindiga sun kai hari kan matafiya a kan hanyar Katsina zuwa Jibiya, sun kashe aƙalla mutum uku.

Wani shaidan da abun ya faru a kan idonsa ya ce maharan sun toshe hanyar, suka kwashi mutanen motoci huɗu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel