'Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Bas, Sun Kashe Direba, Sun Sace Fasinjoji a Katsina

'Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Bas, Sun Kashe Direba, Sun Sace Fasinjoji a Katsina

  • 'Yan bindiga sun hallaka wani direban gwamnatin jihar Katsina na motar zirga-zirgar fasinoji ta KTSTA
  • An ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sace fasinjojin da ke cikin motar bayan kashe direban da ya yi kokarin tserewa
  • Hukumar zirga-zirgar jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma yi karin haske kan wannan hari

Jibia, jihar Katsina - A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan bindiga suka kashe wani direban motar zirga-zirga ta gwamnatin Katsina (KTSTA), Nasiru Yusha’u, bayan da ya yi arba da ‘yan bindiga a kan hanyar Katsina zuwa Jibia.

An ce ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da fasinjojin Yushau bayan sun kashe shi, rahoton gidan talabijin na Channels.

Wani mazaunin kauyen Daddara da ya shaida lamarin da ya faru ya shaida wa gidan talabijin din ta wayar tarho cewa 'yan ta'addan sun far wa motar ne da misalin karfe sha biyu na ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Miyagu sun Bindige Hadimin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Har Lahira

Yadda 'yan bindiga suka sheke dirbea, suka sace fasinjoji sama da 30 a Katsina
'Yan Bindiga Sun Farmaki Mota Bas, Sun Kashe Direba, Sun Sace Fasinjoji a Katsina | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An tattaro cewa Yusha’u ya ga ‘yan bindigan tun farko, sai ya yi yunkurin juyawa, amma ‘yan ta’addan suka kama shi suka harbe shi har lahira.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan kashe direban a nan take, ‘yan ta’addan da ke kan babura suka yi awon gaba da fasinjoji da dama.

Wasu shaidun gani da ido sun ce motar bas din mai dauke da mutane talatin da biyu yawanci ‘yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu daga Kasuwar Jibia zuwa Katsina a lokacin da ‘yan ta’addan suka farmake su.

Da gaske hakan ta faru amma da gyara a maganar, inji KTSTA

A bangare guda, Babban Manaja na Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina, Haruna Musa Rugoji ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai tabbatar da sace fasinjojin ba.

Rugoji ya bayyana cewa, marigayin ya kai fasinjojin da ya dauko daga Katsina zuwa Jibia. Daga nan kuma zai jiyo dasu daga Jibia zuwa Katsina, wanda a kan hanyar dawowa lamarin ya rutsa dashi a Farun Bala.

Kara karanta wannan

Biyan Kudin Fansa ya Jawo aka Lakadawa Fasinjojin Jirgin Kaduna-Abuja Mugun Duka

A cewar wani yanki na batun GM din da TheCable ta rahoto, ya ce ba a sake jin labarin fasinjojin ba, amma yaron motar ya ce ba a sace su ba.

A kalamansa:

“Direban na kokarin juyowa ne da fasinjojin sai ya ga ‘yan bindiga hudu suna tsallaka hanya a wannan yankin. Suka harbe shi har lahira. Watakila suna tunanin zai koma ya ba da labari ne.
“Babu niyyar sace mutane daga ‘yan bindigan saboda ba su yi garkuwa da kowa ba. Sun harbi direban ne kawai suka karbi kudi da wasu wayoyi daga hannun fasinjojin. Ba wani shiri bane.
“Na je wajen da lamarin ya faru kuma ina cikin wadanda suka dauki gawar daga wurin zuwa babban asibitin Katsina a yanzu kuma zuwa Musawa, mahaifar marigayin domin binne shi.”

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ‘yan sandan jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, kuma duk kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ya ci tura.

Kara karanta wannan

Bayan Kuje, ‘Yan ta’adda na Tsara Yadda za su Shiga Wasu Kurkuku 3 a Jihohin Arewa

Jami'an tsaro sun kama mota dauke da bama-bamai a jihar Kano

A wani labarin, rundunar ‘yan sanda a ranar Alhamis ta ce ta kama wasu bama-bamai a cikin wata mota kirar Mercedes Benz da ke kan hanyar Chiranchi a unguwar Dorayi a jihar Kano, rahoton Vanguard.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana hakan a lokacin da yake baje kolin makamai da alburusai da aka kwato tare da gabatar da 'yan ta'adda tare da aka kama da laifuka daban-daban a jihar.

CP Dikko ya ce mutanensa da ke aikin bincike ne suka tare motar domin bincike, yayin da suka kan aikin binciken, wadanda ke cikin motar suka bude wuta kana suka tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.