Peter Obi: Ina cin zabe zan samarwa mutanenmu ayyuka kaca-kaca

Peter Obi: Ina cin zabe zan samarwa mutanenmu ayyuka kaca-kaca

  • Peter Obi ya ci gaba bayyana matsayarsa ta mayar da hankali kan tattalin arzikin kasa da a manufofinsa na zama shugaban kasan Najeriya
  • Obi ya ce idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta sake farfado da kishin kasa na sadaukarwa domin inganta Najeriya
  • Dan takarar na jam'iyyar Labour ya kuma bayyana cewa ta hanyar samar da kayayyakin cikin gida za a samu harkar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, kuma za ta samar da ayyukan yi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Umuahia, jihar Abia - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya sha alwashin tabbatar da ingancin kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa kasashen ketare idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Obi ya yi wannan tsokaci ne a Umuahia, babban birnin jihar Abia, a ranar Asabar, 23 ga watan Janairu, a wajen wani taron addu’o’in da cocin Katolika na Umuahia ya shirya domin yi masa addu’ar nasara.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Najeriya: Ku zabi Tinubu don ci gaba da shan jar miyar da nake baku

Peter Obi ya yi alkawarin yin abin da Buhari bai yiwa 'yan Najeriya ba
Peter Obi: Ina cin zabe zan samarwa mutanenmu ayyuka kaca-kaca | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Ya yi nuni da cewa abin ki ne kuma abin takaici ne a ce miliyoyin ‘yan Najeriya ba su da tabbacin daga inda abincinsu na gaba ke zuwa, duk da cewa kasar na albarkar dimbin albarkatun kasa barkatai.

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Najeriya kasa ce mai fadin murabba’in kilomita 9,23000, kuma tana da yawan mutane miliyan 200. Allah ya azurtamu da man fetur da sauran albarkatu. Muna da mutane sama da miliyan 100 da ke fama da talauci.
“Amma don nuna mu ba kasa mai fitar da kaya ba, a shekarar da ta gabata, jimillar kayan da muka fitar ciki har da mai bai kai dala biliyan 30 ba, shi ya sa ba mu iya samun dala a yau.
“Na shaida wa gwamnan jihar Abia a yau cewa idan na zama shugaban kasa, ina mai tabbatar maka da cewa nan da shekaru biyu kayan da mu ke fitarwa za su inganta domin abin da muke bukata shi ne tallafin gwamnati don jama’ar mu su noma su fitar waje domin samun rayuwa. Hakan zai samar da ayyuka da dama ga jama’armu”.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tinubu ya magantu a kan manyan Bishop-Bishop da aka gani a wajen gabatar da Shettima

2023: Peter Obi ya samu karbuwa sosai a Arewacin Najeriya, in ji Ladi Iliya

A nata bangaren, mataimakiyar shugaban jam'iyyar Labour ta kasa, Ladi Iliya ta ce Obi ya samu karbuwa sosai a Arewacin Najeriya kamar dai takwarorinsa na jam'iyyar PDP da jam'iyyar APC mai mulki.

Ladi ta ci gaba da cewa Obi zai gyara tattalin arzikin kasar nan tare da magance matsalolin tsaro idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023, rahoton Daily Sun.

Ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuli a garin Jos na jihar Filato, yayin wani taron gangami da wayar da kan masu ruwa da tsaki da kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar Labour da ka gudanar.

2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima

A wani labarin, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi batu mai ban dariya a fadarsa da ke Abuja yayin da yake martani ga zabo Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na zaben 2023.

Kara karanta wannan

Dan takarar APC Tinubu: Dole ne na kwaci Najeriya a 2023 don na samar da ayyukan yi

Shugaba Buhari, cikin barkwanci ya ba Tinubu da Shettima kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa, Leadership ta ruwaito.

Buhari wanda ya karbi bakuncin dan takarar mataimakin shugaban kasa jim kadan bayan shugabannin APC da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun kaddamar dashi, ya ce ya yi matukar farin ciki da zabo tsohon gwamnan na jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.