An Kama Wani Kasurgimi Na Ɗaukar Sabbin Yan Bindiga Zasu Kai Hari Gidan Kwamishina a Neja

An Kama Wani Kasurgimi Na Ɗaukar Sabbin Yan Bindiga Zasu Kai Hari Gidan Kwamishina a Neja

  • Hukumar yan sanda reshen jihar Neja ta ce ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da ke shirin sace manyan mutane biyu a jihar
  • Yayin bincike, wanda ake zargi Alhaji Bashiru ya amsa cewa yana shirin sace su ne saboda bashin kudin da yake bi
  • Bayanai sun nuna cewa mutumin ya taɓa aikata kisan kai kuma a kan ɗan uwansa na jini

Niger - Wani ɗan shekara 40, Bashiru Abdullahi, ya shiga hannu bisa zargin ɗaukar mayaƙa yan bindiga da nufin garkuwa da tsohon shugaban ƙasamar hukuma da mahaifin tsohon kwamishina a jihar Neja.

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Neja, Wasiu Abiodun, shi ne ya bayyana haka jiya Asabar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Hukumar yan sanda.
An Kama Wani Kasurgimi Na Ɗaukar Sabbin Yan Bindiga Zasu Kai Hari Gidan Kwamishina a Neja Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A ƙoƙarin da hukumar yan sanda ke yi na kawo karshen ayyukan ta'addanci, yan fashin daji, masu garkuwa da mutane, Kakakin yan sanda ya ce dakarun da ke Caji Ofis a Minna sun yi ram da mutumin bayan samun bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Saki Sabon Bidiyo Yadda Suke Azabtarda Fasinjojin Jirgin Ƙasa, Sun Faɗi Shirin Su

Abiodun ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An kama wanda ake zargi a Kontagora lokacin da yake shiri da ƙoƙarin ɗaukar yan bindiga aiki da nufin aiwatar da garkuwa kamar yadda ya saba."
"Yayin bincike Alhaji Bashiru ya amsa laifinsa da cewa ya shirya garkuwa da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Mariga da mahaifin wani tsohon kwamishona a Neja."

Meyasa zai garkuwa da mutanen biyu?

Abiodun ya ƙara da cewa Mutumin ya ce yanq bin tsohon shugaban ƙaramar hukuma bashin kuɗi N5.8 miliyan kuma da ace ya sace shi ya yi shirin karɓar miliyan N10m na fansa.

A ɗaya bangaren ya ce ya fara shirin sace mahaifin tsohon kwamishina ne saboda ya rike masa kuɗi miliyan N1.5m kuma da ya ci nasara zai karɓi miliyan N15m a matsayin fansa inji shi.

Ya taɓa kashe ɗan uwansa

Kakakin yan sanda ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Haɗin kan ƙasa da tsaron yan Najeriya zan sa a gaba, Buhari ya faɗi abinda zai yi bayan ya sauka mulki

"Da muka ƙara tsananta bincike, ya ce sun haɗa kuɗi da ɗan uwansa har miliyan N79m domin yin wani kasuwanci daga baya ya fara zargin ya zambace shi ne, ya sa sanda ya dake shi a kai hakan ya yi sanadin rasuwarsa."

Amma Alhaji Bashiru ya faɗa wa iyalan gidan su cewa yan bindiga ne suka farmaki shi kuma suka kashe shi a Beri.

A wani labarin kuma EFCC ta bankaɗo yadda Dakataccen Akanta Janar ya karɓi Biliyan N15bn na goro don saurin biyan jihohi 9 wasu kuɗaɗe

EFCC ta ce dakataccen Akanta Janar, Ahmed Idris, ya karbi cin hancin biliyan N15bn don gaggauta biyan kashi 13% na raya yankunan da ake haƙo mai.

Ana ware kaso 13% daga kuɗaɗen shiga na ɗanyen mai domin raya yankuna ta hannun gwamnatocin jihohi 9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262