Shugaba Buhari ya tura da saƙon taya murna da shugaban APC na ƙasa
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jinjina wa shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, yayin da yake cika shekara 79
- A sakon ta ya murnan karin shekara, Buhari ya yaba wa tsohon gwamnan bisa gudummuwar da ya bayar a tarihin Najeriya
- Sanata Abdullahi Adamu, ya cika shekara 79 a duniya, manyan jiga-jigan siyasa musamman na APC sun taya shi murna
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taya shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, murnar Bazday na cika shekararsa 79 a duniya.
Daily Trust ta rahoto cewa shugaban ƙasan ya aike da saƙon murnan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar ranar Asabar.
Buhari ya bi sahun mambobin kwamitin ƙoli na APC ta ƙasa NEC da kwamitin ayyuka NWC da sauran mambobin jam'iyya a kowane mataki domin taya jagoran siyasa murna.
Shugaban ƙasan ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Nasarawa ya kawo kwarin guiwa da hangen nesa ga demokaraɗiyya da tsarin tafiyar da gwamnatin ƙasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, tun a sheakarar 1977 ya fara tsoma hannun sa a siyasa a matsayin mamban majalisar mazaɓu da suka rubuta kundin tsarin mulki. Haka nan yana cikin mambobin taron kundin mulkin ƙasa a 1994.
Rawar da Adamu ke taka wa a APC - Buhari
Bayan haka, Buhari ya jinjina wa shugaban APC na ƙasa bisa kokokarin da yake kan yi na sake fasalin tafiyar da jam'iyyar ta hanyar ba kowa dama da ƙara wa juna ilimi da sauraron kowa.
A cewar shugaban, Adamu ya maida hankali wajen haɓaka demokaraɗiyya a cikin gida, gwamnati mai nagarta da kuma sauke nauyin da Allah ya ɗora masa na tabbatar da yan Najeriya sun samu rayuwa mai kyau.
Haɗin kan ƙasa da tsaron yan Najeriya zan sa a gaba, Buhari ya faɗi abinda zai yi bayan ya sauka mulki
Shugaba Buhari ya roki Allah SWA cikin rahamarsa ya ƙara wa Sarkin Yakin Keffi lafiya, kwarin guiwa, da ƙarfi.
A wani labarin kuma gwamnoni huɗu dake shirin ficewa daga PDP sun gana da juna, sun faɗi matakin da suka dauka na karshe
Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce shi da takwarorinsa uku da suka fusata sun yanke cigaba da zama a jam'iyyar PDP.
Gwamna Wike na jihar Ribas, Gwamna Makinde na Oyo da gwamnan Abiya sun ƙauracewa harkokin PDP tun bayan abun da ya faru.
Asali: Legit.ng