Hotuna da bidiyo: Alkawari ya cika, an daura auren 'Yaradua da Yacine kan sadaki sisin gwal 24
- An daura auren dan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya Umaru Musa 'Yar Adua, Shehu Yar'adua da amaryarasa Yacine Sheriff a Maiduguri
- An daura auren a gidan Sheriff dake da barikin Giwa a Maiduguri inda hamshakai suka samu halartar da suka hada da gwamnoni har da wakilan shugaban kasa
- Sarkin Daura ne ya karbar wa Shehu Yar'adua auren Yacine daga hannun Sarkin Borno kan sadaki sisin gwal 24
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
'Dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'adua, Shehu Yar'adua ya yi wuff da Yacine Muhammad Sheriff a Maiduguri dake jihar Borno a yau Asabar, 23 ga watan Yulin 2022.
An daura auren a gidan Sheriff wanda yake kusa da barikin Giwa kuma ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilci daga ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, Gwamna Babagana Umara Zulum da takwarorinsa na jihar Kebbi da Jigawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kawun amarya kuma tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ya jagoranci wasu jiga-jigai da suka hada da tsohon gwamnan jihar Niger Adamu Mu'azu, tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje, tsohon gwamnan Kastina, Ibrahim Shema, tsohon gwamnan Kebbi, Adamu Aleiro, tsohon gwamnan Bauchi Isa Yuguda, tsohon SGF Yayale Ahmed, tsohon gwamnan Zamfara Ahmed Sani Yarima da kuma shugaban NNPC Mele Kyari da sauransu.
Mai Martaba Sarkin Daura, Umar Faruk Umar ne ya tsaya a matsayin wakilin ango wanda ya karba masa auren daga Shehun Borno, Alhaji Dr. Abubakar Obn Uma Garbai Al-amin a matsayin waliyyin amarya.
An daura auren kan sadaki sisin gwal 24 a gaban shaidu da wakilan amaraya da ango.
Sauran manyan da suka samu halartar daurin aure ta hanyar wakilci akwai tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, wakilan Oba na Beni da wakilan Sarkin Gwandu.
Hotuna da bidiyo: Jiragen saman hamshaƙai 11 sun dira a Maiduguri don bikin ɗan marigayi Umaru Musa Ƴaradua
Asali: Legit.ng