Mijina Bai Iya Soyayya Ba Kuma Ya Watsar Da Ni, Mata Ta Nemi Saki a Kotu

Mijina Bai Iya Soyayya Ba Kuma Ya Watsar Da Ni, Mata Ta Nemi Saki a Kotu

  • Wata mata ta nemi Kotun Kostumare a Abuja ta raba aurenta da mijinta saboda baya nuna mata soyayya kuma ya gudu ya barta
  • Da yake yanke hukunci Alkalin Kotun ya ce duba da rashin jayayya daga mijinta ta raba auren tare da ɗora alhakin kula da yara hannun matar
  • Ta kuma umarci Magidancin mai suna Abubakar ya rinƙa biyan tsohuwar matar N50,000 duk wata na kula yayansa

Abuja - Wata Kotun Kostumari da ke Jikoyi, Abuja ta raba auren da ya shafe shekaru Bakwai tsakanin Lailatu Ayuba da mijinta Abubakar kan rashin kula.

Alƙalin Kotun mai shari'a Labaran Gusau, ya rushe auren bisa hujjar rashin nuna soyayya da kuma zaman lafiya a ciki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Neman Saki a Kotu.
Mijina Bai Iya Soyayya Ba Kuma Ya Watsar Da Ni, Mata Ta Nemi Saki a Kotu Hoto: punchng
Asali: Facebook

Alkalin Kotun ya ce:

"Alamu sun nuna cewa kowane ɓangare ya yi na'am da batun datse igiyoyon auren kuma ita mai ƙara ta roki a bata damar riƙe 'ya'yan da suka haifa kuma wanda ake ƙara bai yi gardama ba."

Kara karanta wannan

Wani Mummunan Ibtila'i Ya Halaka Mata da Miji Da 'Ya'yansu Biyu a Birnin Kaduna

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Duba da wannan, Kotu ba ta da wani zaɓi da wuce ta amince da buƙatun wacce ta kawo ƙara na raba aure da kuma bata damar rike 'ya'yan da suka haifa kasancewar mijinta bai musa hakan ba."
"Bisa haka Kotu ta raba auren kuma ta damƙa kula da yaran hannun matar. Kuma ana umartan ta bar yaran su riƙa zuwa hutun ƙarshen mako da hutu idan sun samu wurin mahaifin su."

Bugu da ƙari Alƙalin ya umarci Magidancin ya rinƙa biyan tsohuwar matarsa N50,000 duk wata wanda zata rinƙa amfani da su wajen ɗawainiyar yaransu.

Meyasa matar da kai ƙara Kotu?

Tun farko dai Lailatu ta kai ƙarar mijinta Abubakar Kotu ne tana rokon a raba auren saboda babu soyayya da kulawa.

Ta faɗa wa Kotu cewa, "Na gaji da zaman auren nan, tun da muka yi aure da Mijina ban taɓa ganin soyayya yadda mata ya dace ace tana samu ba. Ya daina cin abinci na tun da aka ɗaura mana aure, ba ya nuna mun ƙauna"

Kara karanta wannan

Bayan Mijinta Ya Gaza a Gado, Wata Mata Ta Faɗi Yadda Ya Gwada Kwazon Direbanta Har Ya Mata Ciki Sau 2

"Babban abun takaicin shi ne ya watsar da mu ni da 'ya'ya na ya yi tafiyarsa zuwa ƙasar Afirka ta kudu."

A wani labarin kuma Abba Kyari ya gaya wa Kotu Yadda ya tsallake rijiya da baya lokacin harin yan ta'adda a Kuje

Abba Kyari, dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, ya ce ya ɓuya kamar ɓera lokacin harin yan ta'adda a Kuje.

A zaman Kotu na yau Laraba, Kyari ta bakin lauyansa ya sake shigar da bukatar beli, ya ce ya samu damar tsere wa amma ya ƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262