An kuma: Jami'an tsaro sun kama mota dauke da bama-bamai a jihar Kano

An kuma: Jami'an tsaro sun kama mota dauke da bama-bamai a jihar Kano

  • Rundunar 'yan sandan Kano ta ce ta kama wata mota makare da makamai a wani yankin jihar kwanan nan
  • An kwato muggan makamai da suka hada da bindigogi da dama sauran kayayyaki ciki har da wayoyin hannu
  • Rundunar ta kuma bayyana cewa, wadanda ke tuka mmotar motar sun bar ta sun tsere bayan bata-kashi da jami'ai

Dorayi, Kano - Rundunar ‘yan sanda a ranar Alhamis ta ce ta kama wasu bama-bamai a cikin wata mota kirar Mercedes Benz da ke kan hanyar Chiranchi a unguwar Dorayi a jihar Kano, rahoton Vanguard.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana hakan a lokacin da yake baje kolin makamai da alburusai da aka kwato tare da gabatar da 'yan ta'adda tare da aka kama da laifuka daban-daban a jihar.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Mutum 198 sun shiga hannu a Kano, ana zargin 'yan ta'adda ne

Yadda aka kwato makamai a Kano
An kuma: Jami'an tsaro sun kama mota dauke da bama-bamai a jihar Kano | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

CP Dikko ya ce mutanensa da ke aikin bincike ne suka tare motar domin bincike, yayin da suka kan aikin binciken, wadanda ke cikin motar suka bude wuta kana suka tsere.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Alabi Lateef a yayin da jami’an leken asiri da ke sintiri a unguwar Chiranchi Dorayi Kano, a yayin gudanar da bincike sun kama wata mota kirar Mercedes Benz.
"Yayin da suke shirin tsayarwa da binciken motar, sai mutanen da ke cikinta suka bude wa ‘yan sandan wuta, inda jami’an ‘yan sandan suka yi artabu da ‘yan bindigar da suka gudu suka bar motar."

Rahoton da muka samo ya ce, an turo jami'an kunce ababen fashewa, inda suka gano abubuwa masu hadari.

A cewarsa, an gano wadannan abubuwan; bindigogin A47 guda uku dauke da mujallu cike da alburusai casa'in, harsashi goma sha hudu na AK47, hannu daban-daban guda uku da kuma abubuwan fashewa daban-daban (IEDs).

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Sake Kama Wasu Da Suka Tsere Daga Kurkukun Kuje A Jihohin Arewa 2

CP Dikko ya ce:

"Ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi tare kokarin kama 'yan ta'addan."

Ta'addanci na karuwa, 'yan sanda sun kama mutane 198 da ake zargin 'yan ta'adda ne a Kano

A bangare guda, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 20 ga watan Yuli, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Samaila Dikko ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan nasarorin da rundunar ta samu a ranar Alhamis a Kano.

Ya ce 42 daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne da laifin fashi da makami, tara kuma da laifin garkuwa da mutane, 16 da laifin damfara da kuma 27 masu satar motoci da masu satar babura uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.