Hukumar JAMB ta Amince da Rage Makin Shiga Jami’a zuwa 140

Hukumar JAMB ta Amince da Rage Makin Shiga Jami’a zuwa 140

  • Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta yanke makin shiga jami’a a Najeriya zuwa 140
  • Rajestaren JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya ce makarantu suna da 'yancin yanke makin su yadda suke so amma ba zai yi ƙasa da yadda suka yanke ba
  • Oloyede ya ce an yanke makin shiga Polytechnics da Monotechnic zuwa 100 sai kuma makin shiga kwalejojin ilimi zuwa 80.

Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) ta sanya makin shiga jami’a na shekarar 2022/23 zuwa 140 kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.

Rajesteran hukumar Farfesa Is-haq Oloyede ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron bayar da kyaututtuka kan shiga Jami’o’I na shekarar 2022 da aka yi ranar Alhamis a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Wani shugaban APC ya yi ta maza, ya tsere daga hannun 'yan bindiga

Ferfesa Ishak Oloyede ya ce an yanke makin shiga Polytechnics da Monotechnic zuwa 100 sai kuma makin shiga kwalejojin ilimi zuwa 80.

jambito
Hukumar JAMB ta Amince da Rage Maki Shiga Jami’a zuwa 140 FOTO DAILY TRUST
Asali: UGC

Rajistaren JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa makin da aka ambata sune mafi karanci, amma hakan ba yana nufin cewa ba dole sai Makarantu su bi ka’idan su ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce :

"Makarantu suna da 'yancin yanke makin su yadda suke so amma ba zai yi ƙasa da yadda muka yanke ba.

ASUU: Da 'ya'yan 'yan siyasa ne a jami'o'in gwamnati, da yajin mu ba zai kai kwana biyu ba

A wani labari kuma, Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ce idan da ‘ya’yan ‘yan siyasa ne ke halartar jami’o’in gwamnatin Najeriya, yajin aikin kungiyar ba zai shafe kwanaki biyu ba sun shawo kan matsalar tunda ya shafe su.

Kamar yadda shafin jaridar The Cable ta ruwaito, kungiyar ta bayyana cewa wa'adin makwanni biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ministan ilimi Adamu Adamu ya yi yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel