'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Tattara da Dama A Jihar Kogi

'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Tattara da Dama A Jihar Kogi

  • Yan bindiga sun mamayi matafiya sun buɗe wa motarsu wuta a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja, jihar Kogi ranar Laraba
  • Ɗaya daga fasinjojin motar da ya kuɓuta, Benjamin Isaac, ya ce maharan sun tattara baki ɗaya mutum 18 sun yi gaba da su
  • Hukumar yan sanda reshen jihar Kogi ba ta ce komai ba kan harin, amma yan Sakai sun tabbatar

Kogi - 'Yan bindiga sun sace fasinjojin wata Motar Bas mai ɗaukar mutum 18 a ƙauyen Ochonyi-Omoko kan babbar hanyar Abuja-Lokoja a jihar Kogi.

Wani Fasinja da Allah ya kubutar, Benjamin Isaac, ya shaida wa jaridar DailyTrust cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 8:03 na daren ranar Laraba.

Ya ce maharan, waɗan da suka ɓuya a cikin jeji, sun buɗe wa Motar Bas ɗin wuta har suka yi nasarar fasa tayar baya.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Kwata ta yi ajalin wani matashi ɗan shekara 25, Ghaddafi Saleh, a Kano

Babbar hanyar Abuja-Lokoja.
'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Matafiya Wuta, Sun Tattara da Dama A Jihar Kogi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mista Isaac ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun buɗe wa tayoyin baya wuta kuma hakan ya tilasta wa Direban gaza iya shawo kan motar. Lokacin da Direban ya sauka kan hanya, sai yan bindiga suka fito daga inda suke ɓoye suka umarci kowa ya fito, suka ja mu zuwa cikin Daji."

Ya ƙara da cewa ya samu nasarar kuɓuta daga hannun masu garkuwan tare da wasu fasinjojin yayin da suka tsere cikin daji.

Isaac ya ce ya hau motar ne a kan hanya a Zuba, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Okpella a jihar Ondo.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Wani mamba a ƙungiyar yan Bijilanti, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya tabbatar da lamarin da cewa ya ji ƙarar harbin bindiga yana tsaka da Alwalar Sallan Isha'i.

"Bayan kammala sallah ne na gaggauta sanar da abokan aikina, muka haɗa tawaga zuwa wurin, nan ne fa muka ga Motar Bas a gefen hanya babu kowa a ciki."

Kara karanta wannan

Yadda na tsallake rijiya da baya lokacin harin yan ta'adda a Kuje, Abba Kyari ya magantu a Kotu

Ya ce daga baya suka gane Fasinjojin Motar aka sace kuma yanzu haka Yan sa'akai sun bazama cikin jejin domin gano inda maharan suka yi da kuɓutar da mutanen.

Kakakin hukumar yan sanda na jihar Kogi, DSP Williams Ovye Ayah, bai amsa kiran waya ko sakonnin da aka tura masa kan harin ba.

A wani labarin kuma Yan ta'addan ISWAP sun saki sabon bidiyon yadda suka yi babbar Sallah, sun yi barazanar kai hare-hare

Ƙungiyar ISWAP ta saki wani sabon Bidiyo na yadda mambobinta suka gudanar da bikin babbar Sallah da ta gabata.

Ƙungiyar wacce ta yi ikirarin kai hari gidan Yarin Kuje, ta yi barazanar kai hare-hare gidajen Yarin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262