Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro a Abuja
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron tsaro a fadar gwamnati da ke birnin tarayya Abuja yau Alhamis
- Manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan na Sojojin ƙasa, sama da ruwa, Sufetan yan sanda da sauran su duk sun samu halartar taron
- Taron na zuwa ne a dai-dai lokacin da tsaro a Najeriya ke ƙara taɓarɓarewa musamman a arewacin ƙasar
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron majalisar koli ta tsaro a fadar gwamnati da ke babban birnin tarayya Abuja, ranar Alhamis.
Buhari, Sallau, babban mai taimaka wa shugaban kasa ta fannin kafafen sada zumunta ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar haɗe da Hotuna a shafinsa na Tuwita.
"Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jagoranci taron tsaro a gidan gwamnati ranar 21 ga watan Yuli, 2022," inji sanarwan.
Taron ya samu halartar Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari, da kuma mai ba da shawar kan harkokin tsaro na ƙasa, Babagana Monguno.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Babban Hafsan tsaro na ƙasa, Janar Lucky Irabor, shugaban sojin ƙasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo da shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Isiaka Oladayo Amao, duk sun halarci taron.
Sauran mahalarta taron sun haɗa da, Sufeta Janar na yan sanda, Usman Alƙali Baba, Darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya (DSS), Yusuf Bichi, da kuma daraktar hukumar tsaron fasaha, (NIA), Ahmed Rufai Abubakar.
Hotunan taron tsaron na yau
A wani labarin kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan sauya sheƙar gwamna Matawalle daga PDP zuwa jam'iyyar APC
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman ta a birnin Shehu ta ce babu ta yadda gwamna zai rasa kujerarsa saboda ya sauya sheka zuwa wata jam'iyya.
Da take yanke hukunci, ta tabbatar da hukuncin farko da babbar Kotun tarayya ta Gusau ta yanke kan gwamna Bello Matawalle.
Asali: Legit.ng