Da Dumi-Dumi: Masu Gidajen Burodi Za Su Tsinduma Yajin Aiki Na Kasa Baki Daya A Najeriya
Kungiyar masu gidajen burodi ta 'Premium Breadmakers Association of Nigeria (PBAN) da ta kunshi direktoci da masu hadin gwiwa ta kammala shirin fara yajin aikin gargadi na kwana hudu daga ranar Alhamis 21 ga watan Yulin 2022.
Masu gidajen burodin sun dauki wannan matakin ne don kokawa kan hauhawar farashin kayan yin burodi a kasar suna cewa aiki na gagararsu a kasar, rahoton Daily Trust.
Bugu da kari, sun bukaci hukumar NAFDCA ta rage kudin tara wato N154,000 da ta ke karba ga kamfanonin burodi wadanda ba su sabunta lasisinsu ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PBAN ta kuma yi kira ga gwamnati ta bawa mambobinta bashi masu saukin ruwa da babban bankin kasa, CBN, ke bawa kanana da matsakaitan yan kasuwa (MSMEs).
Kungiyar ta kuma bukaci a rage yawan hukumomi da ke sa ido kan ayyukan masu gidajen burodin.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng