Kaddamar Da Shettima: Hotunan Yadda Matasan Najeriya Suke Zolayar APC Da Gasar #BishopChalllenge a Tuwita

Kaddamar Da Shettima: Hotunan Yadda Matasan Najeriya Suke Zolayar APC Da Gasar #BishopChalllenge a Tuwita

  • Wasu yan Najeriya sun fara #BishopChallenge a Twitter don zolayar APC bayan an rahoto cewa jam'iyyar mai mulki ta dauko hayan fastoci don taron
  • Hotunan gasar ba komai bane illa abin dariya kwana guda bayan hotunan fastocin ya janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta
  • Gasar yana ta tashe a dandalin sada zumunta ta Twitter inda dubban mutane ke ta baza hotunan wadanda suka shiga gasar

FCT, Abuja - Wasa matasan Najeriya sun fara wani gasa da suka yi wa lakabi da #BishopChallenge domin zolayar jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Hotuna da bidiyon Bishop Bishop da fastoci a wurin taron kaddamar da dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Kashim Shettima, a ranar Laraba 20 ga watan Yuli ne suka janyo gasar.

Bishop wurin kaddamar da Shettima
Kaddamar Da Shettima: Hotunan Yan Najeriya Da Suka Fara Gasar #BishopChallenge Don Zolayar APC. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Ku Dena Yin Sojan Gona Da Sunan Mu, CAN Ta Gargadi Yan Siyasan Najeriya

Tunda farko, hotunan fastocin a taron da APC ta yi a birnin tarayya Abuja, ya janyo cece-kuce tsakanin wasu yan Najeriya.

Amma, wasu matasa yan Najeriya sun zabi yi wa abin kallo na nishadi kuma suka fara gasa domin zolayar jam'iyyar mai mulki da mutanen da ake zargin ta dako hayansu ne.

Wasu daga cikin hotunan sun yi farin jini sosai ana kuma ta baza su.

Wasu cikin wadanda suka shiga gasar sun bayyana cewa su magoya bayan Peter Obi ne, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party.

Kwangiri ne a kansa...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164