Abin da bincike ya bayyana game da Abba Kyari da Sauransu, Shaidan NDLEA
- Bincike ya bayyana sinadarin da aka kama a hannun dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari Hodar Iblis ne
- Abba Kyari da wasu mutane hudu sun bayyana a gaban babban kotun tarayya dake Abuja saboda ci gaba da shariar zargin badakalar miyagun kwayoyi
- An gwada duka sinadarin da aka samu a hannun Abba Kyari a dakin gwaje-gwaje dake jhar Legas
Jihar Osun - Wani shaida a shari’ar da ake yi wa dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP) Abba Kyari, ya ce gwajin da aka yi wa sinadarin da aka gano a hannun Abba Kyari, ya nuna cewa hodar iblis ce. Rahoton PREMIUM TIMES
Kyari da wasu mutane hudu da suka hada da ACP Sunday Ubua, ASP Bawa James, Insifeto Simon Agirigba , da John Nuhu sun bayyana a harabar babban kotun tarayya a Abuja kan zargin badakalar miyagun kwayoyi
A rahoton Daily Trust, mai gabatar da kara na biyu, Abubakar Zekeri Aliyu, da lauyan su tare da daraktan shari’a na hukumar NDLEA na kasa, Sunday Joseph suka jagoranci gabatar wa kotu shaidan a cikin ambulan mai dauke da karar NDLEA/FCTC/010/2021.
A cewar shaidan, wanda Sufeto ne a hukumar NDLEA, an gwada dukkan sanadarin ne a dakin gwaje-gwaje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An mika sinadarin ne ga kwararriyar mai bincike, Misis Patricia Afolabi dake Legas, a ranar 7 ga watan Febrairu, 2022 inda aka gano hodar iblis ne aka samu a hannun Abba Kyari.
DCP Abba Kyari da mutum 6 sun bayyana a kotu, za a gurfanar da su
A wani labari kuma, Abba Kyari da wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen badakalar miyagun kwayoyi sun bayyana a harabar babban kotun tarayya a Abuja.
The Nation ta kawo rahoto a safiyar Litinin, 7 ga watan Maris 2022 cewa DCP Abba Kyari sun shigo kotu, ana sauraron a gurfanar da su a gaban Alkali.
Asali: Legit.ng