Idan dama taki: Gwamna zai gayyaci bokaye da 'yan bori a jiharsa su fatattaki 'yan ta'adda
- Gwamnatin Anambra ta gano wata sabuwar dabara na yakar rashin tsaro da sauran laifuka a fadin jihar
- Gwamna Chukwuma Charles Soludo na jihar Anambra ya yanke shawarar amfani da bokaye da yan bori don taimakawa gwamnatinsa wajen yakar miyagu
- Za a yiwa masu maganin gargajiya da yan bori rijista kuma za su daina hadawa miyagu surkullen nasara a ta’addanci
Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta kammala shirye-shirye don yiwa bokaye da yan bori rijista a jihar don hana su yiwa masu garkuwa da mutane da sauran
Gwamnatin Anambra ta yanke shawarar neman taimakon masu maganin gargajiya da yan bori a kokarinta na yakar rashin tsaro da sauran laifuka masu alaka a jihar.
Tuni gwamnatin jihar ta kammala shirye-shirye don yiwa bokaye da yan bori rijista a jihar kuma an kulla yarjejeniya da su kan su daina yiwa masu aikata laifuka asiri musamman layun da ake amfani da su wajen sace mutane.
Jaridar The Nation ta rahoto cewan an yanke wannan hukuncin ne a yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar wanda Gwamna Chukwuma Charles Soludo ya jagoranta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwamishinan labarai na jihar, Sir Paul Nwosu, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 20 ga watan Yuli, a garin Awka bayan taron, ya ce gwamnatin na son yin amfani da wannan tsarin ne wajen kawar da masu mugun zuciya a jihar.
Ya yi bayanin cewa bayan an gano cewa wasu bokaye na samar da layu wanda da su ne yan bindiga suke aiki, don haka ya zama dole a kidaya su tare da yi masu rijista a matsayin masu aiki da aka kasa zuwa masu maganin gargajiya da yan bori.
“Yayin da gwamnati ta yaba da cewar wasu na bayar da gudunmawa ga kiwon lafiya, tana kuma sane da cewar suna taimakon wadannan miyagu da asirin da ke karfafa masu gwiwar aikata muggan laifuka.”
A cewar Nwosu, wadannan laifuka sune garkuwa da mutane, karbar kudin fansa, fille kawunan mutane da sauransu, inda yace a duk inda aka samu irin wannan laifuka, cikin sauki za a iya zakulo su daga rijistan.
Rundunar yan sanda ta ayyana neman shugaban yan bindiga, Ado Aleru, ruwa a jallo
A wani labari na daban, rundunar yan sandan jihar Katsina ta ayyana neman gogarmar dan bindiga, Ado Aleru, wanda Sarkin Yandoto na Zamfara ya nadawa sarautar Sarkin Fulani a ranar Asabar ruwa a jallo.
Ana neman Aleiro ne kan zargin aikata ayyukan ta’addanci ciki harda kashe akalla mutane 100, jaridar Vanguard ta rahoto.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Zamfara ta dakatar da Sarkin Yandoton Daji, Aliyu Marafa, kan nadawa dan ta’addan da ake nema ruwa jallo sarauta.
Asali: Legit.ng