Kano: Dakin Ajiya Da Wasu Wurare Sun Kone Kurmus A Gobarar Data Tashi a Makarantar Yaran Ma'aikatan Jamiar BUK

Kano: Dakin Ajiya Da Wasu Wurare Sun Kone Kurmus A Gobarar Data Tashi a Makarantar Yaran Ma'aikatan Jamiar BUK

  • Gobara ta tashi a wani gini na makarantar frimare ta yaran ma'aikatan Jami'ar Bayero ta Kano da ke old site inda dakin ajiya da bandaki suka kone kurmus
  • Sanarwar da mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta Jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ta tabbatar da hakan
  • Abdullahi ya ce sun samu kiran neman dauki ne a yammacin ranar Talata kuma suka tura jami'ai nan take don zuwa kashe gobarar, kawo yanzu ba a gano dalilin wutar ba

Jihar Kano - Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce wuta ta lalata dakin ajiye kaya da kuma bandaki a makarantar frimari ta yaran ma'aikatan jami'ar Bayero ta Kano a old site.

Hakan na cikin wata sanarwa ne da mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya fitar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Sabuwar cuta ta bullo a wata makaranta, mutum 10 sun jikkata, 1 ya mutu

Motar Kashe Wuta
Kano: Dakin Ajiya Da Wasu Wurare Sun Kone Sakamakon Gobara Da Ta Tashi a Makarantar Yaran Ma'aikatan Jami'a. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Ya ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata kamar yadda The Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Abdullahi:

"Mun samu kiran neman dauki misalin karfe 5.53 na yamma, daga wani Halliru Bello kuma nan take muka aike da tawagar mu ta bada dauki zuwa wurin misalin karfe 5.58 domin tsayar da wutar daga bazuwa zuwa wasu ajijuwa.
"Wani ginin mai fadin 200ft da 200ft da ake amfani da shi matsayin makarantar yaran ma'aikatan jami'a, da ke dauke da ofishin hedimasta, dakin hutawan malamai maza da malamai mata sun dan kone kadan yayin da wani dakin ajiya da bandaki sun kone baki daya saboda gobarar.
"A halin yanzu ana bincike domin gano dalilin afkuwar gobarar," in ji shi.

Bauchi: Mummunan Gobara Ta Lakume Shaguna 42 a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa

A wani rahoton, a kalla shaguna 42 ne suka kone a Student Centre, ta Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, sakamakon gobara da ta yi sanadin asarar dukiyoyin miliyoyin naira.

Kara karanta wannan

Nasara: Tsageru sun sha ragargaza yayin da suka farmaki sansanin soji a jihar Neja

Shagunan da suka kone a Block D suna bayan dakin kwanan dalibai mata ne a Yelwa Campus na jami'ar kamar yadda The Punch ta rahoto.

Shagunan da gobarar ta yi wa barna sun hada da shagunan kwamfuta da shagunan aski a shagunan sayar da kayan masarufi da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164