Matasan Kirista a Najeriya Sun Bukaci INEC Ta Kara Tsawaita Kwanakin Rajistan Zabe

Matasan Kirista a Najeriya Sun Bukaci INEC Ta Kara Tsawaita Kwanakin Rajistan Zabe

  • Matasan kungiyar kiristocin Najeriya, YOWICAN, sun roki Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na Kasa, INEC, ta tsawaita kwanakin rajistan zabe
  • Owoyemi Olushola, Shugaban YOWICAN na yankin Arewa maso tsakiya ne ya yi wannan rokon yayin taron wani manema labarai a birnin tarayya, ranar Talata
  • Olushola ya ce dukkan yan Najeriya na da yancin su yi rajistan zaben sannan ya roki INEC ta kai cibiyoyin rajistan zabe kusa da karkara domin mutane su samu daman yin rajistan cikin sauki

Abuja - Reshen matasa na Kungiyar Kirista ta Najeriya, YOWICAN, ta Arewa maso tsakiya ta yi roko ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta tsawaita kwanakin rajistan karin zabe don kada a dakilewa mutane damar yin zaben.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Babu Gudu Babu Ja Da Baya' ASUU Ta Dora Wa Ministan Kwadago Laifin Tsawaita Yajin Aiki

Matasan CAN.
Matasan Kirista Sun Bukaci INEC Ta Kara Tsawaita Kwanakin Rajistan Zabe. Hoto: @nannews.
Asali: Twitter

Owoyemi Olushola, Shugaban YOWICAN na Arewa maso tsakiya ne ya yi wannan rokon yayin taron manema labarai mai taken: "Ba mu amince da tikitin musulmi da musulmi ba" a ranar Talata a Abuja, rahoton NAN.

A cewarsa, INEC ta kuma matsar da cibiyoyin rajistan zaben zuwa ga mutanen karkara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina son in shiga jerin masu kira ga cewa a tsawaita kwanakin yin rajistan katin zabe. Don Allah, INEC ta yi kokari ta tsawaita kwanakin zaben.
"Muna addu'a da fatan za su yi hakan saboda kowa na da damar ya yi rajistan," in ji shi.

Ya yi kira ga kowa da kowa musamman Kirista su fito su kada kuri'a a zaben na shekarar 2023, su zabi wanda suke so' don ganin yadda kasar za ta cigaba.

Olusola ya kuma yi kira gare su da su rika bibiyar wakilansu a dukkan matakai don sa ido kan ayyukan da ya kamata su yi.

Kara karanta wannan

2023: Ba Za Mu Bari Mambobin Mu Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba, In Ji Matasan Kungiyar CAN

Shugaban INEC ya saurari muryar mutane mafi rinjaye da ke rokon tsawaita kwanakin rajista.

Muna fatan INEC za ta saurari bukatun mu, in ji shi.

Tsohon Shugaban Kungiyar Kirstocin Najeriya, CAN, Ya Zama Dan Takarar Mataimakin Gwamna a Najeriya

A wani rahoton, kun ji an zabi tsohon shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, a Jihar Kwara, Rabaran Joshua Olakunle, a matsayin dan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben 2023, rahoton This Day.

Rabaran Olakunle wanda ya fito daga Ora a karamar hukumar Ifelodun, zai yi takara ne tare da Mr Hakeem Oladimeji Lawal, wanda ya yi nasarar zama dan takarar jam'iyyar a zaben cikin gida na ranar 31 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164