Hotunan daliban sakandare a Najeriya zaune dirshan a kasa suna rubuta jarabawa ya janyo cece-kuce

Hotunan daliban sakandare a Najeriya zaune dirshan a kasa suna rubuta jarabawa ya janyo cece-kuce

  • Wasu hotunan daliban makarantar sakandare a jihar Ogun suna zaune dirshan a kasa yayin rubuta jarabawar canjin aji sun janyo cece-kuce
  • Kamar yadda wani lauya mai suna Festus Ogun ya wallafa, yace 'yan makarantar St. Kizito's High School ne dake Iwopin a yankin Waterside
  • Ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata, 18 ga watan Yulin 2022 a jihar Ogun sakamakon halin ko in kula da gwamna ya nunawa ilimi

Ogun - Hotunan daliban makarantar St. Kizito’s High School, dake Iwopin, a yankin Ogun Waterside a jihar Ogun zaune a kasa dirshan suna rubuta jarabawar canjin aji ya bazu kuma ya janyo maganganu.

Lauya Festus Ogun, wanda ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 18 ga watan Yulin 2022.

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

Daliban Ogun
Hotunan daliban sakandare a Najeriya zaune dirshan a kasa suna rubuta jarabawa ya janyo cece-kuce. Hoto daga Festus Ogun
Asali: Facebook

A tare da tsokacin da yayi a wallafar, ya kara da likau mai cewa #DapoMustGo, ma'ana Dapo dole ya tafi.

Wallafar tace: "Daliban makaranta St. Kizito’s High School, dake Iwopin, a yankin Ogun Waterside ta jihar Ogun suna rubuta jarabawar canjin aji inda suke zaune dirshan a kasa a yau ranar 18 ga watan Yulin 2022. Ina taya Prince Dapo Abiodun murna kan wannan nasarar da ya samu."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Martanin jama'a

Tuni masu kishin al'umma da ilimi a Najeriya suka fara martani. Ga wasu daga cikin martanin da Legit.ng ta tattaro muku:

Adefemi Adeniyi: "Me shugabanninmu na siyasa suke yi? Sun gaza kuma sun ci amanar jama'ar yankin Ogun Waterside."
Comr Akinbote Taiwo: "Barista, kana nufin babu dalibi da yake da wurin zama ko guda daya? Ina tantama amma za a iya yi min bayani in gamsu. Ina shawartar masu taimako, PTA da SBMC na al'ummar da su gaggauta daukar mataki domin ceto shugabanninmu na nan gaba."

Kara karanta wannan

Nasara: Tsageru sun sha ragargaza yayin da suka farmaki sansanin soji a jihar Neja

ASUU: Hotunan dalibin da ya bude gidan cin abinci, shi ke girkawa kuma yake siyarwa

A wani labari na daban, wani matashi dalibin Najeriya ya bayyana yadda rayuwa ta juya masa bayan kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'in Najeriya sun tsunduma yajin aiki.

Ya sanar da cewa, shi alheri wannan yajin aikin ya zame masa saboda ya yi amfani da lokacinsa yadda ya dace.

Ya yanke hukuncin yin amfani da zaman gida na dolen ta hanyar siyar da abinci a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng