Daga fita siyo mata shawarma, Budurwa ta yi awon gaba da Motar Saurayinta a Kano
- Wata budurwa ta shiga hannun dakarun yan sanda bisa zargin sace Motar Saurayinta a Kofar Fanfo da ke cikin birnin Kano
- Saurayin ya bayyana cewa daga zuwa sayo mata Shawarma da ya dawo ya taras ba motar kuma ba labarinta a wurin
- Budurwar mai suna Ilham ta yi wa yan sanda bayanin gaskiyar abin da ya faru, da dalilinta na ɗauke motar
Kano - Wata zankaɗeɗiyar budurwa mai suna, Ilham, ta shiga hannu bisa zargin sace Motar Saurayinta daga zuwa a Sayo mata Shawarma a Anguwar Ƙofar Fanfo, kan titin jami'ar BUK a cikin birnin Kano.
Aminiya ta rahoto cewa mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya tabbatar da kama budurwar ga manema labarai.
Yanzu-Yanzu: Shahararriyar jarumar Fim a Najeriya ta yanke jiki ta faɗi, ta rasu tun kafin zuwa Asibiti
Kiyawa ya ce Saurayin da aka sace wa motar a ranar 12 ga watan Yuli, 2022, ya yi gaggawar kai rahoton ɓatan motarsa ga hukumar yan sanda.
Meyasa ta ɗauke masa mota?
Bayan jami'an yan sanda sun yi ram da ita, Ilham ta bayyana cewa ta ɗauke motar sahibinta ne saboda tana binsa bashin kuɗi N150,000, kuma take-takensa sun nuna ba zai biyata ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Budurwar ta ce ganin ba shi da niyyar biyan bashin da take binsa, shiyasa ta yanke shawarin ɗauke motarsa.
Ta ya har budurwan ta ɗauke motar?
Da yake bayyana yadda aka sace motar, Saurayin ya bayyana cewa sun haɗu da masoyiyarsa a Hauren Wanki, inda ta faɗa masa yunwa take ji kuma ba abun da take sha'awa sai shawarma.
"Daga fita na sayo mata abinda ta ke son ci, na dawo na taras ba motar ba labarin ta bare kuma wacce ke ciki," inji shi.
Ilham ta ƙara da cewa wani Saurayinta na daban ta kira ya ɗauke motar ya aje mata kuma ta yi haka ne domin kudin da take bin mai Motar.
Bayanai sun nuna cewa tuni jami'an yan sanda suka garzaya suka kamo saurayin da ya ɗauke motar domin cigaba da bincike.
A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje ya hana amfani da Adidaita sahu da daddare a jihar Kano
Gwamnatin Kano ta sanar da dokar hana ayyukan Keke Napep bayan ƙarfe 10:00 na dare kuma zata fara aiki ranar Alhamis.
Hakan ya biyo bayan yawaitar amfani da yan Adidaita sahu wajen aikata muggan laifuka a jihar, a cewar kwamishinan labarai.
Asali: Legit.ng