Gwamna Masari: Gwamnati Da Hukumomin Tsaro Sun Gaza Tsare Yan Najeriya
- Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce gwamnati da hukumomin tsaro sun gaza sauke nauyin tsare yan Najeriya
- Masari ya ce daya daga cikin abubuwan da ya janyo matsalar rashin tsaron shine mutuwar jami'an tsaro da dama da suka hada da yan sanda da sojoji
- Gwamnan na Katsina ya ce an samu cigaba a yaki da ta'addancin amma ba a kai inda ake so ba yana mai fatan za su magance matsalar kafin mika gwamnati
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Katsina - Aminu Bello Masari, gwamnan Jihar Katsina, ya ce gwamnati ta gaza samarwa yan Najeriya tsaro, rahoton The Cable.
Masari ya bayyana hakan ne cikin wata hira da BBC Hausa ta yi shi da aka wallafa a ranar Talata.
Ya ce mutane sun dogara ga gwamnati da jami'an tsaro ne domin su kare su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Jami'an tsaro da mu gwamnati wanda mutane suka dogara da mu don kare su, kuma mun gaza wurin yin hakan," in ji Masari.
"Amma idan ka duba dalilin gazawar, an kashe jami'an tsaro da yawa. Bai kai sati biyu ba; an kashe kwamishinan yan sanda; an kashe sojoji, jami'ai sun rasa rayyukansu a kokarin magance rashin tsaro.
"Ba Katsina kadai rashin tsaro ya shafa ba, ya shafi kusan kowacce jiha a Najeriya da wasu kasashen da muke makwabtaka kamar Nijar da Mali su ma suna fama da lamarin.
"An samu cigaba ba kamar baya ba, amma ba mu kai inda muke so ba kuma muna addua ga Allah ya bamu ikon magance rashin tsaro kafin mu mika mulki ga gwamnati a gaba."
Jihar Katsina na cikin jihohin da ke fama da rashin tsaro.
A ranar 5 ga watan Yuli, yan bindiga sun bude wa tawagar Shugaba Muhammadu Buhari wuta a kusa da karamar hukumar Dutsinma a jihar.
Tawagar jami'an tsaron na hanyarta ne na zuwa Daura don shirin zuwan shugaban kasar lokacin da aka kai mata harin.
Asali: Legit.ng