CJN Tanko Yayi wa Alkalai Martani Bayan Sun Zargesa da Shan Jar Miya Shi Kadai

CJN Tanko Yayi wa Alkalai Martani Bayan Sun Zargesa da Shan Jar Miya Shi Kadai

  • Babban alkalin kotun koli ya yi martani ga alkalai 14 da suka zargesa da laifin rashawa tare da tauye musu hakkinsu a matsayinsu na alkalai amma shi yana waddaka yadda yaso
  • A wata wasikarsu sun koka a kan rashin canza motocin ma'aikatar da suka sukurkuce, karancin wutar lantarki, karin kudin harajin wutar lantarki, rashin sabis din yanar gizo da sauransu
  • Sai dai, yayin martani CJN din yace gari ne ya dauka zafi, tare da bayyana dalilan da yasa yake tattalin arzikin ma'aikatar shari'ar yadda ya dace don gujewa fadawa halin rashi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Shugaban alkalan Najeriya, Ibrahim Muhammad, ya yi martani ga alkalan da suka zargesa da rashawa.

Daily Trust ta ruwaito yadda alkalai 14 suka tura wa Muhammad wasika, wanda suka yi ikirarin ya dauki tsawon lokaci yana tauye musu hakkinsu.

Kara karanta wannan

Borno: An Fallasa Dabarju, Mai Tatsar Wutar Fitillun Kan Titi Yana Kaiwa Gidan Kankararsa

CJN Tanko Muhammad
CJN Tanko Yayi wa Alkalai Martani Bayan Sun Zargesa da Shan Jar Miya Shi Kadai. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Alkalan sun ce horarwan da ake musu na lamurran waje duk bayan shekara, ana yi ne don inganta alkalancin kasar, sai dai Muhammad ya toshe wannan kafar.

Manyan abubuwan da alkalan suka fi damuwa dasu a wasikunsu ta kwamitin walwala sune;

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rashin maye gurbin lalatattun motoci; matsalar matsugunni; rashin magunguna a asibitin kotun koli; matsalar wutar lantarki a kotun kolin; karin kudin harajin wutar lantarki; rashin karin alawus din diesel; rashin sabis din yanar gizo ga mazauna da wuraren shari'a.

Haka zalika, sun kara da cewa yayin da CJN din yake tura 'yan uwa da abokan arzikinsa kasashen ketare, kadan ne daga cikin alkalan da ke karkashin Muhammad ke samun wannan damar.

Sai dai, yayin martani a wata takarda, wacce Ahuraka Yusuf Isah, hadiminsa ya fitar a madadinsa, na biyar a daraja a fadin kasar ya bayyana yadda ya yi nasarar tattalar arzikin kotun yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Mutum 10 sun mutu, 5 sun hallaka a harin 'yan ta'adda a jihar Benue

"Shugaban alkalan Najeriya, Mai girma Alkali Ibrahim Tanko Muhammad zai so ya tabbatar da cewa ya samu wasikar da 'yan uwansa na kotun koli alkalai suka rubata gami da mikawa garesa."
"A kowanne yanayi ana ganin alkalai ne ba tare da sauraronsu ba, wannan shivne ya bayyana dalilin da yasa CJN ya ki shiga sabgar har zuwa lokacin da wata wasika, wacce ba rufaffiya ce ta fara yaduwa a cikin al'umma. Matsayin wannan wasikar daidai yake da kwasar rawa tsirara a cikin kasuwa garemu.
"Tabbas kotun koli bata aiki a waje, sannan hakan ya shafi tattalin arzirki da wayewar yanayin siyasar kasar. Baya ga haka, yanayin kotun ta dauki tsawon lokaci tana rayuwa a kan turbar kundin tsarin shari'arta.
"Idan aka yi wani kasafi, yana kunsar bangarori biyu, abun da ke aukuwa da asalin jarin, sannan duka biyun ina kasafta su zuwa abubuwa. Gwamnatin tarayya ke sakin kasafi bayan dubi ga abubuwan da kasafin ya kunsa. Kuma laifi ne amfani da kudin wani abu a wani abu daban.

Kara karanta wannan

Kana zuwa Turai da iyalanka amma ka hanamu zuwa: Alkalan kotun koli sun kalubalanci Shugaban Alkalai

"Zargin da ake a takaice shi ne an yi, an yi da yawa ko kuma ya kamata a ce an yi gaba daya ba wai babu abun da aka yi ba; wanda shi ne abun da ya dace a halin da kasarmu take ciki.
"Kafin nan an nada alkalai takwas a shekarar 2020 a kotun, babu wani karin kasafi da aka samar don sabbin ofisoshi tare da ma'adanar littafan da suka dace, amintaccen tallafi, matsugunni mazauna da sauran abubuwan da suka dace garesu.
"Hakan yasa kotun ta yi amfani da abubuwan da take da su a kasa don cimma bukatunsu. Akalla dukkan alkalan wannan kotun suna da mataimakansu, sai dai idan wasu sun bukaci kari," yace.

Ya kara da cewa:

"Yanzu an nada Alkaliya Aina a kotun FCT Abuja watan da ya gabata, yayin da dayar Barista Ramatu ta rasu watanni uku da suka wuce. Yanzu haka ma'aikatar shari'a na kokarin ganin yadda za a nada wasu mataimakan alkalai da sauran mataimakan ma'aikata a wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun sako shugaban kauye don ya tara N100m ya karbi mutanensa 30

"Baya ga haka, alkalan kotun koli biyu sun rasu cikin wannan lokacin da ake maganar. Gaba daya hudun da suka yi ritayar da biyun da suka rasu sun ja kotun ta kashe wasu kudade a matsayin garatutu da alawus."

A takaice dai Tanko ya bayyana cewa, zargin da ake masa ba gaskiya bane, kasar ce take a haka kuma yake tattali tare da mafi da abinda aka bada domin hidindimun da suka dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel