Wata mata ta maka tsohon mijinta gaban Kotun Musulunci kan ya auri babbar ƙawarta

Wata mata ta maka tsohon mijinta gaban Kotun Musulunci kan ya auri babbar ƙawarta

  • Wata mata a Kaduna, Fisdausy Musa, ta garzaya Kotun Musulunci ta kai ƙarar tsohon mijinta bayan ya auri babbar ƙawarta
  • Matar ta zargi tsohon mijin, Saidu Abubakar, da mallaka wa sabuwar amaryarsa kayanta na aure da akwatuna
  • Mutumin ya musanta dukkan zargin da tsohuwar matar take masa ta bakin lauyansa, Alƙali ya ɗage zaman domin a gabatar da shaidu

Kaduna - Wata mata yar shekara 25, Firdausy Musa, a ranar Litinin, ta kai ƙarar tsohon mijinta, Saidu Abubakar, gaban Kotun Shari'ar Musulunci a Kaduna saboda ya auri babbar ƙawarta.

Mai ƙara ta bakin lauyarta, Zainab Murtala, ta zargi wanda suke ƙara da damƙa akwatunanta da kyaututtukanta ga sabuwar amaryarsa, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Gudumar Kotu.
Wata mata ta maka tsohon mijinta gaban Kotun Musulunci kan ya auri bababr ƙawarta Hoto: Dailynigerian.com
Asali: UGC

A jawabinta, Firdausy ta gaya wa alƙali cewa:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shahararriyar jarumar Fim a Najeriya ta yanke jiki ta faɗi, ta rasu tun kafin zuwa Asibiti

"Ba mu jima da yin aure ba amma ba mu taɓa tare wa a wani gida na tsawon watanni biyu ba, ya fi gane ya kama mana Hotel mu haɗu a can."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ana haka ne ya danna mun saki ɗaya, daga baya muka sasanta kuma ya sake saki na, daga nan kuma sai ya je ya auri babbar ƙawata, ya mallaka mata duk kayayyaki na haɗi da kayan sawa na."

Ta roki Kotun ta taimaka mata wajen dawo mata da kayan aurenta haɗi da wanda ta siya da kanta lokacin da ta je Umrah Saudiyya.

Matar ta ƙara da tabbatar wa Alƙalin cewa ba ta taɓa neman Mijin nata ya sake ta ba lokacin da suke tare, kamar yadda Jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shin Mijin ya amsa laifinsa?

A ɓangarensa, wanda ake ƙara ta bakin lauyansa da ya wakilce shi, Abubakar Sulaiman, ya musanta bai wa tsohuwar matarsa wata kyauta a rayuwar auren su.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sallami baki ɗaya hadimansa daga kan kujerunsu saboda abu ɗaya

Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Rilwanu Kyaudai, ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 9 ga watan Agusta, 2022 domin gabatar da shaidu.

A wani labarin kuma kun ji cewa An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina

Yan sanda sun yi ram da Kamala Abubakar a wata maboyar masu aikata laifuka dauke da wasu kayan laifi a yankin Ɗanmusa.

Yan ta'adda da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai hari Kuje, inda suka kwance yan ta'addan da ake tsare da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262