Da dumi-dumi: Kamfanin jirgin sama mafi dadewa a Najeriya ya dakatar da aiki bisa dalilai
- Kamfanin jirgin Najeriya mafi dadewa ya bayyana dakatar da ayyukansa a kasar bisa tsadar manyan fetur na jirage
- Najeriya na fuskantar tsadar man fetur tun farkon shekarar nan, lamarin da ke tunzura sana'o'i da kamfanoni
- A bangare guda, ma'aikatan jiragen sama sun bayyana goyon baya da shiga yajin aikin ASUU saboda wasu dalilai
Najeriya - Kamfanin jiragen sama mafi dadewa a Najeriya, Aero Contractors, ya dakatar da aiki na wani dan lokaci bisa matsalar tattalin arziki.
Idan baku manta ba, kamfanonin jiragen sama na ta kokawa kan tashin farashin man jiragen sama da aka fi sani da Jet A1 da kuma fama da karancinsa.
A baya-bayan nan ne dai Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Najeriya (AON) ta yi hasashen cewa nan ba da dadewa ba wasu kamfanonin jiragen sama guda biyu za su daina aiki saboda karancin Jet A1 da sauran kalubalen aiki da ya sa kamfanonin jiragen shiga firgici.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana ci gaban, kamfanin ya ce dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Yuli, rahoton Daily Trust.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar This Day ta samu labarin cewa, mummunan yanayin da kamfanin jirgin ya shiga ya ta'azzara ne sakamakon tsadar man jiragen sama, lamarin da ke zama barazana ga ayyukan sauran kamfanonin dakon kaya da jirage na cikin gida.
Kamfanin jirgin, wanda ke aikin jigilar man fetur da iskar gas shekaru da yawa kuma ya tashi zuwa aikin jigilar mutane tun 2000 ya sha fama da bashin kusan Naira biliyan 50.
Yajin aiki: Ma'aikatan jiragen sama zasu rufe filayen jirage don taya ASUU nuna fushi
A wani labarin, kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta Najeriya (ANAP), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen yajin aikin da ASUU ta shiga yi ko kuma za su rufe bangaren sufurin jiragen sama tare da hada kai da malaman jami’o’in.
A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ANAP, Kwamared Abdulrasaq Saidu ya fitar, ya bukaci shugaban kasa Mohammadu Buhari da ya kawo karshen yajin aikin ba tare da bata lokaci ba, rahoton Leadership.
ANAP ta lura cewa ci gaba da zama a gida da daliban manyan makarantu ke yi na kara haifar da munanan dabi’u a kasar nan yayin da dalibai ke yin wasu abubuwa marasa kyau da ke iya lalata makomarsu.
Asali: Legit.ng