Ministan Buhari Ya Gujewa Zaben Gwamna a Jiharsa Ya Shilla Jamus

Ministan Buhari Ya Gujewa Zaben Gwamna a Jiharsa Ya Shilla Jamus

  • Ministan Harkokin Cikin Gida kuma tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola ya gujewa zaben gwamnan Jihar Osun ya tafi Jamus
  • Hadimin ministan a bangaren watsa labarai, Jane Osuji, ta tabbatar da cewa Aregbesola a halin yanzu baya Najeriya, ya tafi wakiltar Najeriya a wani taro a Jamus
  • Gwamnan Osun na yanzu Gboyega Oyetola ba su shiri da ministan duk da cewa shine ya yi masa shugaban ma'aikatan fada sannan ya gaji kujerar gwamnan bayan Rauf ya kammala wa'adinsa

Tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya gujewa zaben gwamna da ake yi a jihar Osun.

Jaridar Daily Trust tattaro cewa Aregbesola, wanda a halin yanzu ya ke takun saka da tsohon shugaban ma'aikatan fadarsa kuma magajinsa, Gboyega Oyetola, a halin yanzu yana Jamus.

Kara karanta wannan

Jita-jitar barin APC: Hadimin Farfesa Yemi Osinbajo ya fito, ya fadi gaskiyar lamari

Rauf Aregbesola
Aregbesola Ya Gujewa Zaben Gwamna a Jiharsa Ya Shilla Jamus. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan jarida sun tafi akwatin zabensa a Ilesha, suka gano cewa Ministan Harkokin Cikin Gidan ba zai yi zaben ba.

Hadimin Aregbesola ya tabbatar ministan ya yi balaguro

Hadimin ministan a bangaren watsa labarai, Jane Osuji, ta tabbatarwa Daily Trust cewa Aregbesola a halin yanzu baya kasar.

A cewarta, Ministan yana Jamus yana wakiltar Najeriya a wani taro.

Sola Fasure, hadimin Aregbesola, ya shaidawa majiyar Legit Hausa cewa ministan bai samu ikon zuwa Osun ba saboda takaita zirga-zirga.

Fasure ya ce Aregbesola ya tafi hallartar wani aiki.

Zaben Osun: Ni Zan Ci Zabe, In Ji Oyetola Bayan Ya Kada Kuri'arsa

A bangare guda, Gboyega Oyetola, gwamnan Jihar Osun, ya ce shi mutane za su sake zaba.

Da ya ke magana da manema labarai bayan ya jefa kuri'arsa a ranar Asabar, Oyetola ya ce mutane 'suna sane' kuma sun ga bukatar su fito su yi zaben, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kwankwaso ya zabi fasto matsayin mataimaki a zaben 2023 mai zuwa

Gwamnan ya ce idan har ba a boye-boye a harkar, babu bukatar a rika bi ana cewa mutane su yi zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164