Dalilin da ya sa muka kai wa ayarin motocin Tinubu hari a Legas – Wanda ake zargi
- Jami'an tsaro sun kama wadanda suka kai wa ayarin motocin Bola Ahmed Tinubu hari a jihar Legas
- Mataimakin sufeto-Janar na Yansanda Bode Adeleke ya ce jami'an su za su sa kaimi wajen farautar wanda ya dauki nauyin kai wa Tinubu hari
- Daya daga cikin wadanda su kai wa Tinubu hari ya ce a biya su kudi su hana ayarin motoci Tinubu zuwa gidan Oba na Legas
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Legas - Jami'an tsaro sun kama wasu ‘yan kungiyar asiri daban-daban har guda 8 da laifin kai wa ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, hari a Legas. Rahoton Daily Trust
Wadanda ake zargin, shugabannin kungiyoyin daban-daban a jihar Legas, sun amsa laifin su inda suka ce biyan su aka yi domin su aikata barnan.
A ranar 20 ga watn Yuni ‘yan daba sun kai hari kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu a jihar Legas.
Daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Ramon Aniseoju, ya ce an dauke su ne domin su kawo cikas ga ayarin motocin, da kada su bari su kai ga inda za su je.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"An biya mu ne don hana wadanda ke cikin ayarin su isa fadar sarki ‘Oba na Legas’.
Jami’in mai kula da shiyya ta 2 da ta kunshi jihohin Legas da Ogun, Bode Adeleke, mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda, wanda ya gabatar da wadanda ake zargin, ya ce, sun amsa cewa su ‘yan kungiyar asiri ne tare da bayyana sunan wanda ake zargi da daukar nauyin harin.
Ya ce nan ba da dadewa ba za a kamo mai laifin, inda ya ce ‘yan sanda sun kara kaimi wajen farautar su.
Yan Bindiga Sun Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Jihar Filato
A wani Labari, Wasu ‘yan bindiga sun yi wa tawagar sojoji kwanton bauna a kauyen Zurak Kampani da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato. Rahoton Daily Trust
‘Yan bindigar, a cewar mazauna yankin, sun isa unguwar ne a lokacin da mazauna yankin ke gudanar da harkokin kasuwa.
Asali: Legit.ng