Kaduna: El-Rufa'i' Ya Bada Umurnin A Ɗauki Sabbin Malamai 10,000 Bayan Ya Kori 2,000
- Malam Nasir El-Rufa'i, gwamnan jihar Kaduna ya ba wa hukumar KADSUBEB umurnin daukan sabbin malaman makaranta 10,0000
- Shugaban KADSUBEB, Tijjani Abdullahi, ya ce za a bude shafin intanet na rajistar neman aikin daga ranar 21 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta
- Wannan umurnin daukan sabbin malaman na zuwa ne bayan KADSUBEB ta sallami malamai fiye da 2,000 a baya bayan nan kan fadi jarrabawa
Jihar Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufa'i na Jihar Kaduna ya bawa hukumar Ilimi bai ɗaya na Jihar Kaduna, KADSUBEB, ta dauki sabbin malamai 10,000.
Tijjani Abdullahi, shugaban KADSUBEB ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar a ranar Juma'a, The Cable ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdullahi ya ce za a bude shafin daukan malaman na tsawon makonni biyu daga 21 ga watan Yulin, 2022, ya kara da cewa Jami'ar Jihar Kaduna, KASU, ce zata tsara shafin na intanet.
"Waɗanda suka cancanta za su iya neman aikin da satifiket na ilimi, NCE, daga makarantu da aka amince da su, masu digiri a bangaren Ilimi (B.Ed, B.A EED, B.Sc, Bd, B.Tech a kowanne bangare daga jami'a amintaciya) suma suna iya nema," a cewar sanarwar.
" Za a bude shafin na tsawon sati biyu daga ranar da aka fara rajistar wato 21 ga watan Yulin 2022, zuwa 5 ga watan Agustan 2022 lokacin da za a rufe.
"Za a tantance wadanda suka nema kuma a gayyaci wadanda suka yi nasara zuwa yin jarrabawa ta Kwamfuta a cibiyoyi uku; Kaduna, Zaria da Kafanchan."
"Wadanda suka ci maki 75% da abin da ya yi sama ne za a gayyata mataki na gaba.
"Ana sa ran wadanda suka yi nasarar su taho da takardun karatunsu na ainihi da kwafi yayin interview. Za a duba na ainihin yayin da kwafin za a bawa masu tantancewa."
"Hukumar zata bada tukwici ga wadanda za a tura ƙauyuka inda akwai karancin malamai da suka nema, ko wadanda suka yi nasara."
Wannan sanarwar daukan malaman na zuwa ne bayan KADSUBEB ta sallami fiye da malamai 2,000 saboda fadi jarrabawar cancanta.
Mun Kori Malamai 2,357 Ne Don Habbaka llimi, In Ji Gwamnatin Jihar Kaduna
A wani rahoton, Gwamnatin Jihar Kaduna, ta yi martani kan korar malaman frimare guda 2,257 daga jihar, The Nation ta rahoto.
Gwamnatin Jihar, a cikin makonni da suka gabata, ta kori fiye da malamai 2,000 ne makarantun firamare saboda rashin kokari da cancanta.
Ta kuma kori shugaban kungiyar malamai, NUT, na Jihar Kaduna saboda rashin rubuta jarrabawar sanin makamashin aiki da ta wajabtawa malamai.
Asali: Legit.ng