'Yan Bindiga Da yan ta'adan Ansaru sun fafata a jihar Kaduna
- Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ‘yan kungiyar ta’addar Ansaru hari a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna
- Yan kungiyar Ansaru sun shawarci jama’a da su samu makaman kare kansu daga makiya da yaki da gwamnati domin kafa daular Musulunci
- Kungiyar Ansaru ta samu nasarar kare kanta daga harin da yan bindiga suka kai mata saboda muggan makaman da take dashi
Jihar Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ‘yan kungiyar ta’addar Ansaru hari a karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna. Rahoton Daily Trust
Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan kungiyar suna yin wa’azi ga jama’ar yankin ne a lokacin da ‘yan bindiga suka bude wuta, inda suka kashe yan kauyen biyu.
An ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Damari da ke karkashin gundumar Kazage a Gabashin karamar hukumar a kokarinsu na fatattakar ‘yan ta’addan Ansaru daga kauyen.
Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan Ansaru da suka mamaye Gabashin karamar hukumar Birnin Gwari, ke koya wa mutanen kauyukan kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ishaq Usman Kafai, shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an dauki tsawon sa’a guda ana arangama tsakanin kungiyoyin biyu.
A cewarsa, ‘yan kungiyar Ansaru dake dauke da muggan makamai sun yi galaba a kan harin ‘yan bindigar wanda hakan ya sanya su (’yan bindiga) suka gudu daga kauyen.
“An samu barna a yayin arangamar; an kona wani shago; motoci biyu sun kone; An kona wani Asibiti mai zaman kansa. ‘Yan bindigar ma sun kashe wasu ‘yan unguwar (ma’aikata) guda biyu yayin da ‘yan fashin ke guduwa cikin dajin,” inji shi.
Ya ce ‘yan kungiyar ta Ansaru sun cigaba da wa’azin bayan fafatawar, inda suka shawarci jama’a da su samu makamai don kare kansu daga makiya tare da yaki da gwamnati domin kafa abin da suke kira daular Musulunci.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya yi alkawarin jin hakikanin abin da ya faru daga yankin ‘yan sanda kafin ya yi tsokaci.
Buhari na neman a kafa kotun yaki da cin hanci da rashawa a Afrika
A wani labari kuma, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne zakaran yaki da cin hanci da rashawa na nahiyan Afrika, ya bukaci a kafa wata kotun kasa da kasa da za ta hukunta masu laifi. Rahoton Daily Nigeria
Ya kuma bukaci shugabannin kasashen Afirka da su kara zage damtse wajen yaki da cin hanci da rashawa, tare da samar da karin abubuwan da za su hana satar kudaden jama'a.
Asali: Legit.ng