Kamfanin jirgin Max Air zai fara jigilar maniyyata 16,000 zuwa Najeriya a ranar Asabar

Kamfanin jirgin Max Air zai fara jigilar maniyyata 16,000 zuwa Najeriya a ranar Asabar

  • Kamfanin jirgin sama na Max Air zai fara jigilar maniyyata 16,000 daga Kasar Saudiyya zuwa Najeriya ranar Asabar
  • Max Air shahararren kamfanin jirgin sama ne wanda babban ofishin su yana cikin jihar Kano tare da sansaninsa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano
  • Hukumar NAHCON ta ware maniyyata 16,000 daga jihohi 13 zuwa kamfanin Max Air domin gudanar da aikin hajjin Bana

Hajji Bana - Daya daga cikin masu jigilar maniyyata aikin Hajji na shekarar 2022, Max Air, ya ce zai fara jigilar maniyyata daga kasar Saudiyya zuwa Najeriya a ranar Asabar. Rahoton Daily Nigeria

Max Air Kamfanin jirgin sama ne wanda hamshakin dan kasuwa Alhaji Dahiru Barau Mangal ya kafa shi a shekarar 2008, babban ofishin kamfanin yana cikin jihar Kano tare da sansaninsa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano.

Kara karanta wannan

Limamin JIBWIS, Sheikh Umar Maigona, ya rasu a kasar Saudiyya bayan kammala aikin Hajji

Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Ibrahim Dahiru, ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, ya ce mahajjata daga Borno ne za a fara jigilar su zuwa gida.

pILGRIMS
Kamfanin jirgin Max Air zai fara jigilar maniyyata 16,000 zuwa Najeriya ranar Asabar FOTO VANGUARD
Asali: Twitter
"Max Air na son tabbatar wa daukacin alhazai 16,000 da ya yi jigilarsu zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin hajjin bana na alkawarin dawo da dukkan su cikin kankanin lokaci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewa:

"Kamfanin jirgin na son sanar da mahajjatan cewa ya kara wani Boeing 747-400 a cikin jiragensa domin kwashe dukkan mahajjatan gida lafiya."

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ware maniyyata 16,000 daga jihohi 13 zuwa kamfanin Max Air domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2022.

Jihohin sun hada da Borno, Adamawa, Bauchi, Gombe, Taraba, Kogi, Niger, Kwara, Jigawa, Katsina, Benue, Plateau da Nasarawa.

Kara karanta wannan

2023: Na sanyawa Tinubu da Shettima albarka, in ji Ali Modu Sheriff

Zaben Osun : Ba Aikinmu Bane mu hana Siyar da Kuri'u, Inji Kwamishinan INEC

A wani labari kuma, Jihar Osun - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba aikinta ba ne hana sayen kuri’u a lokacin zabe.

Kwamishinan Zabe na INEC a Jihar Osun, Farfesa Abdulganiy Raji, ya bayyana haka a lokacin da yake magana a gidan Talabijin na Channels Television na Daily Sunrise a safiyar ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel