2023: Zabe Ya Fi Zuwa Coci Da Masallaci, In Ji Jarumin Najeriya Kanayo. O. Kanayo

2023: Zabe Ya Fi Zuwa Coci Da Masallaci, In Ji Jarumin Najeriya Kanayo. O. Kanayo

  • Anayo Modestus, shahararren jarumin fina-finan Najeriya da aka fi sani da Kanayo. O. Kanayo ya ce zabe ya fi zuwa coci da masallaci
  • Jarumin wanda ya yi fice a masana'antar ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram don fadakar da yan Najeriya muhimmancin zabe
  • Kanayo ya ce duk wani dan Najeriya da bai samu katin PVC na zabe ba yana cikin matsalar kasar don haka kada mutane su ce kuri'arsu ba za ta yi tasiri ba

Fittacen jarumin Nollywood, Anayo Modestus, wanda aka fi sani da Kanayo. O. Kanayo, ya ce a ra'ayinsa samun katin zabe na PVC ya fi zuwa coci da masallaci.

Jarumin ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Instagram inda ya wallafa bidiyo yana bayani cewa kowanne dan Najeriya na da ikon ceto kasar. Jarumin ya ce duk wani kasa da bai samu katin PVC ba yana cikin matsalar kasa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda budurwa ta cancarawa saurayinta aski mai kyau ya girgiza intanet

Kanayo O Kanayo.
2023: Zabe Ya Fi Zuwa Coci Da Masallaci, In Ji Jarumin Najeriya Kanayo. O. Kanayo. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Ya kara jaddada cewa yin zabe ya fi zuwa coci da masallaci saboda ba addu'a bane kadai ko hayaniya a dandalin sada zumunta amma zuwa jefa kuri'a ne a zahiri ne ake zaben dan takara.

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ni da ku muna da ikon ceto kasarmu. Babu wanda zai maka. Kada ka ce ba za a kirga kuri'arka ba. Farko, ka tafi ka yi zabe. Zuwa yin zabe ya fi zuwa coci da masallaci. Ku fahimce ni, babu sunan Almasihu a wurin zabe.
"Shi yasa kuke addu'a a sunan Almasihu, suma suna yi. Ba a zabe a dandalin sada zumunta. Aiki ne na zahiri. Idan kawo yanzu baka da katin zabe na PVC, ka zama cikin matsalar Najeriya. Na fada maka wannan."

Lauyan, wanda ya zama jarumi ya shiga jerin jarumai da dama irinsu Falz, Davido, MI Abaga, Peter Okoye (P Square), Mr Macaroni da sauransu da suka bukaci yan Najeriya su mallaki PVC.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Kanayo yana daya cikin fitaccen jarumai na Nollywood, ya shafe shekaru da dama a masana'antar kuma ya fito a fina-finai kamar 'Lion Heart' da labarai mai dogon zango da ya samu lambar yabo 'Living in Bondage'.

Ga bidiyon a kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164