Ganduje Ya Yi Wa Babachir Lawal Martani: Gidauniya Ta Bata Taba Tilastawa Kirista Karbar Musulunci Ba
- Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi martani da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal kan zarginsa da amfani da gidauniyarsa tun tilasta wa kirista karbar musulunci
- Ganduje ya karya wannan zargi da Babachir, yana mai cewa abin takaici ne irin wannan karya ta rika fitowa daga bakin mutum kamar tsohon SGF din
- Gwamnan na Kano ya ce gidauniyarsa ta mayar da hankali ne wurin tallafawa al'umma musamman marayu, gajiyayyu, masu bukata ta musamman da sauransu kuma tana mutunta yancin kowa ya yi addininsa
Kano - Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya yi watsi da ikirarin da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya yi na cewa ana amfani da Gidauniyar Ganduje don tilastawa Kirista karbar Musulunci.
Yayin da ya ke nuna kin amincewarsa da zabin Kashim Shettima a matsayin mataimakin Asiwaju Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC, Lawal ya yi zargin Ganduje na neman musuluntar da Najeriya.
Tsohon SGF din ya yi ikirarin cewa an kirkiri gidauniyar ne musamman domin tilastawa kirista shiga musulunci kamar yadda The Punch ta rahoto.
Amma, cikin sanarwa da kwamishinan labarai na Kano, Malam Muhammad Garba ya fitar, a madadinsa, Ganduje ya ce babu gaskiya cikin kalaman na Babachir.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Babu tilas a addini, Ganduje
Ya ce duk da cewa babu tilas a addini, musulunci ta bawa kowa zaben addininsa, kuma ta bawa wadanda ba musulmi ba hakkokinsu na tattalin arziki, al'adu da mulki.
Ya ce babu wani lokaci da gidauniyar ta tilastawa wani kirista ko wanda bai yi imani ba karbar musulunci domin hakan ya saba da koyarwar musulunci.
"Abin takaici ne lokacin da kasa ke bukatar hadin kai don cigaba da hakuri da addinai, mutum kamar Babachir, wanda ake girmamawa, zai yi karya ba tare da la'akari da matsayinsa a APC ba sa kusancinsa da dan takarar mu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu."
"Idan aka yi la'akari da ayyukan ta, gidauniyar ba ta addini bane sai dai tallafawa al'umma, wadanda ba musulmi ba ma suna amfana da ayyukan da ta ke yi.
"An kafa Gidauniyar Ganduje ne shekaru 40 da suka shude kuma tana ayyukan taimako da jin kan al'umma da suka hada da bada magunguna, tallafi da taimako ga mabukata a cikin jama'a musamman marayu da masu bukata ta musamman, bada taimakon magunguna ga masu ciwon sukari, hawan jini, zazzabin cizon sauro, ciwon hakori da mazu juna biyu da wadanda suka haihu," in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa gidauniyar ta gina makarantu da cibiyoyin lafiya masu yawa, ta raba kayan makaranta da kayan koyon karatu da gina rijiyoyin burtsatsai da masallatai da raba abinci lokacin sallah da azumi.
Gwamnan, a cewar sanarwar ya ce tikitin musulmi da musulmi ba zai janyo a yi watsi da hakkin kiristoci ba.
An kuma yi kira ga tsohon SGF din da sauran yan Najeriya su rika kula da abubuwan da suke furtawa musamman kan harkar addini.
Babban Sallah: Coci A Kaduna Ta Raba Abinci Ga Musulmi Mabukata Da Marayu, Ta Yi Rabon Kudin 'Barka Da Sallah'
A wani rahoton, wani coci mai suna The Christ Evangelical and Life Intervention Fellowship Ministry ta raba abinci ga musulmi mabukata da marayu don murnar babban sallah.
Cocin ta kuma ce ta bada kyautan kudi na "Barka da Sallah" ga yara domin karfafa dankon zumunci tsakanin musulmi da kirista a jihar, rahoton The Cable.
Yayin rabon kayan, Yohanna Buru, shugaban cocin ya ce abu ne mai muhimmanci a taimakawa musulmi mabukata su yi bikin sallah cikin murna.
Asali: Legit.ng