Kyawawan hotunan Ango AGF Malami da amaryarsa Nana Hadiza Buhari sun bayyana

Kyawawan hotunan Ango AGF Malami da amaryarsa Nana Hadiza Buhari sun bayyana

  • Kyawawan hotunan sabon ango AGF Abubakar Malami, da dalleliyar amaryarsa, Nana Hadiza sun bayyana
  • A ranar Juma'a, 8 ga watan Yulin 2022 ne aka daura auren Malami da Hadiza a wani kebantaccen biki a Abuja
  • Kyakyawar amarya Nana Hadiza Buhari ita ce ta uku a gidan Malami bayan uwargida Aisha da ta tsakiya Fatima

Antoni janar na tarayya, AGF Abubakar Malami ya auri diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Nana Hadiza Buhari a ranar Juma'a, 8 ga watan Yulin 2022.

Nana Hadiza mai shekaru 41 ita ce diyar shugaban kasan ta uku da marigayiyar tsohuwar matarsa, Safinatu.

Abubakar Malami da Nana Hadiza
Kyawawan hotunan Ango AGF Malami da amaryarsa Nana Hadiza Buhari sun bayyana. Hoto daga @hausaroom
Asali: Instagram

Nana Hadiza ta taba auren Abdulrahman Mamman Kurfi wanda suka haifa 'ya'ya shida da shi kafin rabuwar aurensu.

A halin yanzu, Nana Hadiza ita ce mace ta uku a gidan Malami bayan Aisha uwargida da Fatima ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotunan barka da sallah daga gidan ango Lilin Baba da amaryarsa Ummi Rahab

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kyawawan hotunan amarya Hadiza da Ango Abubakar Malami sun bayyana kuma sun matukar birge jama'a.

Hotuna: Jerin kyawawan 'ya'ya 4 da shugaba Buhari ya aurar bayan hayewarsa mulki

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aurar da 'ya'yansa hudu tun bayan hayewarsa madafun iko a shekarar 2015.

Uku daga cikin bukukuwan an yi su ne cike da shagali, bidiri tare da aji irin na manya. Daya daga ciki ne kadai aka yi shi ba tare da wani gagarumin shagali ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng