Hotuna: Jerin kyawawan 'ya'ya 4 da shugaba Buhari ya aurar bayan hayewarsa mulki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aurar da 'ya'yansa hudu tun bayan hayewarsa madafun iko a shekarar 2015. Uku daga cikin bukukuwan an yi su ne cike da shagali, bidiri tare da aji irin na manya. Daya daga ciki ne kadai aka yi shi ba tare da wani gagarumin shagali ba.
Zahra Buhari da Ahmad Indimi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada auren diyarsa, Zahra Muhammadu Buhari ga 'dan gagarumin 'dan kasuwa, Muhammad Indimi.
An daura auren a ranar 16 ga watan Disamban 2016 inda aka dinga shagali babu kama hannun yaro.
Hanan Buhari da Muhammad Turad Sha'aban
A ranar 4 ga watan Satumban 2020 aka daura auren Aisha Hanan Buhari da kyakyawan angonta, Muhammad Turad Sha'aban, 'dan tsohon 'dan majalisar tarayya na jihar Kaduna.
Hotuna da Bidiyo: Dandazon jama'a sun fito nuna wa Buhari kauna yayin da yake takawa zuwa gida daga idi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saboda fama a lokacin da ake yi da cutar korona, an yi bikin a fadar shugaban kasa ba tare da tsananta gayyata ba inda aka kayyade masu halartar bikin.
Yusuf Buhari da Zahra Bayero
'Da namiji daya tilo na shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kyalla ido ya hango zukekiyar 'yar gidan sarauta, jinin marigayi Sarki Ado Bayero na Kano.
Babu bata lokaci Buhari ya aike da wakilai aka nema wa Yusuf auren Zahra Bayero, wanda aka daura a ranar Juma'a, 20 ga watan Augustan 2021 kan sadaki N500,000 a fadar mahaifinta dake garin Bichi.
Nana Hadiza Buhari da Abubakar Malami
A ranar Juma'a, 8 ga watan Yulin 2022 ne aka daura auren Nana Hadiza Buhari da angonta, AGF Abubakar Malami, a fadar shugaban kasa dake Abuja.
An gano cewa, an yi takaitaccen biki wanda 'yan uwa ne yawanci suka samu halarta.
Kyawawan Hotunan Buhari da Yusuf a Filin Sallar Idin Babbar Sallah Sun Kayatar
A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhanmadu Buharui ya garzaya garinsu, Daura dake jiha Katsna tun ranar Juma'a domin yin hutun babbar sallah a can.
A ranar Asabar, 9 ga watan Yulin 2022 ne aka yi babbar sallah wacce take daidai da rana 10 ga watan Dhul Hijja. Musulmai daga dukkan fadin duniya sun sallaci sallar idin babbar sallah.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ma ba a bar shi a baya ba tunda ya garzaya masallacin Kofar Arewa tare da 'yan uwa Musulmi inda yayi sallarsa ta Idi.
Asali: Legit.ng