2023: Tinubu ya dauki Musulmi a matsayin abokin takara, CAN ta yi martani
- Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta ce ba za ta marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Tinubu, baya ba idan ya zabi abokin takara Musulmi
- Mataimakin babban sakataren CAN, ya ce kungiyar addinin ba za ta kuma marawa duk dan takarar shugaban kasa Kirista da ya zabi Kirista a matsayin abokin takara
- A halin da ake ciki, gwamnan jihar Kano ya ce Tinubu ya yarda zai dauki Musulmi a matsayin abokin takararsa don gaje Buhari a 2023
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Daga karshe dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya amince da daukar Musulmi a matsayin abokin takararsa gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli, a yayin bikin babban Sallah a jihar, Daily Independent ta rahoto.
Tinubu ya dauki Alhaji Kabir Ibrahim Masari, dan siyasar Katsina, a matsayin mataimaki na wucin gadi domin cike wa’adin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta diba masa.
Ganduje yayin da yake zantawa da kimanin malamai 100 a gidan gwamnati daga wani bangare da bikin Sallah ya ce an shawarci Tinubu da ya dauki Musulmi a matsayin abokin takara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Mun shawarce shi da ya dauki mataimaki Musulmi kuma ya amince. Tikitin Musulmi da Musulmi gaskiya ne. ba sabon abu bane a Najeriya,” in ji gwamnan na Kano.
Ya kuma bukaci malaman da su yiwa Tinubu addu’a don ya zama shugaban kasar Najeriya a 2023.
Abokin takara Musulmi: CAN ta yi martani
A halin da ake ciki, kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta jadadda hukuncinta na kin goyon bayan dan takarar shugaban kasar APC, Tinubu, a babban zaben 2023 tunda alamu masu karfi sun nuna zai dauki abokin takara Musulmi, Vanguard ta rahoto.
Jaridar ta bayyana cewa CAN ta yanke hukuncin ne yayin da manyan masu ruwa da tsaki na arewa suka yanke shawarar daukar Musulmi don sanar da shi a hukumance.
Da yake martani ga tikitin Musulmi-Musulmi, Elder Biodun Sanyaolu, mataimakin babban sakataren CAN, ya yi Allah wadai da lamarin, yana mai cewa mambobinsu ba za su marawa yunkurin baya ba.
Kan ko Tinubu ya isa ga kungiyar, Sanyaolu ya ce:
“Tukuna, CAN ta bayyana matsayinta cewa ba za ta marawa tikitin Musulmi da Musulmi baya ba haka kuma tikitin Kirista da Kirista.
“Ba wai batun tikitin Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista bane game da rashin yardar ke tsakaninmu ne tsawon shekaru bakwai da suke wuce wanda ya munana harma ga kungiyar addinai ta Najeriya, NIREC.
“Abun da muke fadi kuma muke so shine shugaban da zai yi kokari ga kowa, ba tare da la’akari da matsayi, addini, jinsi, yanki, launin fata da sauransu ba.
“Abun da kawai muke muradi shine shugaba da zai yi adalci ga dukkanin Kiristoci, Musulmai harda ga yan gargajiya. Talauci bai san addini ba.
“Idan akwai harin bam zai kashe duk wanda ke hanyarsa ne ba tare da la’akari da addini ba. Muna son shugabanci mai kyau da zai yi adalci ga kowa da shugabanci mai kyau a Najeriya.”
Za mu yi maraba da Tinubu idan ya zo gare mu, in ji Sanyaolu
Da yake magana kan ko kungiyar za ta saurari APC idan kamfen ya fara, Sanyaolu ya ce:
“Idan ya zo, za mu karbe shi hannu bibbiyu sannan mu duba abun da suka tanadarwa yan Najeriya da jama’a.”
Tinubu ya yanke shawara, ya zabi abokin takararsa – Kwamitin kamfe
Mun ji cewa Sanata Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya yanke shawarar akan wanda zai zaba a matsayin abokin takararsa kama yadda jaridar VANGUARD ta rawaito.
Wata majiya mai karfi a kungiyar yakin neman zaben Tinubu da ta bukaci a sakaya sunanta ta tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.
Majiyar ta ce Tinubu zai bayyana sunan dan takarar a wannan makon.
Asali: Legit.ng