Kanawa Sun Karkata Zuwa Layya Da Rakuma Saboda Tsadar Raguna Da Shanu A Bana

Kanawa Sun Karkata Zuwa Layya Da Rakuma Saboda Tsadar Raguna Da Shanu A Bana

  • Mutanen Kano da dama sun kauracewa raguna da shanu sun rungumi rakuma don yin layya a babban sallah ta 2022
  • Wani mai sayar da shanu a kasuwar Kano ya ce bai taba ganin tashin farashin raguna da shanu irin na wannan sallah ta bana ba
  • Dan'azumi Alka, wani mai sayar da rakuma ya ce yana ganin mutane sun karkata ga rakuma ne a bana domin farashinsu ya fi sauki kuma sun fi nama

Masu sayar da rakuma suna ta murmushi suna soke kudadensu a aljihu a yayin da mazauna Kano ke tururuwa zuwa siyan rakuma don farashin raguna, wanda aka fi layya da su ya yi tashin gwauron zabi.

A ranar Juma'a, a kasuwar Kofar Na'isa da ke Kano, Premium Times ta lura cewa masu sayar da rakuma sun mamaye wuraren da a baya masu sayar da raguna da shanu suke.

Kara karanta wannan

Trela Ta Markade Mutum 8 Da Ragunan Sallah Masu Yawa A Wani Mummunan Hatsari

Rakuma a Kano
Kanawa Sun Karkata Zuwa Layya Da Rakuma Saboda Tsadar Raguna Da Shanu A Bana. Hoto: @Premiumtimesng.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani wurin sayar da raguna, Idris Illiyasu, dilallin raguna daga Sokoto, ya koka da karancin kasuwa. Ya ce tsadar kudin ragon ne yasa ake wuyan samun masu siya.

Iliyasu ya ce farashin raguna suna farawa ne daga N40,000 zuwa N105,000. Ya ce ragunan da ake sayarwa N105,000, a bara an sayar da su kan N90,000.

Ragunan da ake sayarwa N50,000, a bara N35,000 aka sayar da su, in ji shi.

"Abin mamaki game da kasuwar raguna na bana shine babu ribubi a yayin da sallah ke karatowa, kamar shekarun baya.
"A yayin da sallah ke matsowa, farashin rago bai sako ba kuma masu siya suna raguwa," in ji Illiyasu.
"Ni shafe fiye da shekaru 10 ina dillancin shanu, amma bana na ga tsadar raguna da ban taba gani ba," Illiyasu ya kara.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Musulmai a duniya na amfani da raguna don yin layya ne a lokacin babban sallah, saboda lada da ke tattare da hakan idan an kwatanta da wasu dabobi.

An fi son yin layya da rago idan mutum na da hali, dabban da ke biye da shi wurin daraja shine shanu.

Musulunci ya kuma bada damar yin layya da dabobi kamar tunkiya, akuya, ko bunsuru wanda sun fi sauki idan aka kwantanta da rago, shanu ko rakumi.

Ko da mutane sun hada kudi sun siya shanu, kudin na da yawa.

Yayin da masu sayar da raguna ke kokawa, masu sayar da rakuma suna ta farin ciki domin mutane na siya. Dan'azumi Alka, dilalin rakuma ya ce mutane na siyan rakuma domin sun fi sauki.

Akasin shanu, rakuma sun fi sauki saboda irin ciyayin da suke ci, rakuma na iya rayuwa suna cin ciyawa da ganye kuma za su iya shafe lokaci mai tsawo ba tare da cin abinci ko shan ruwa ba.

Kara karanta wannan

Ragon layya N300K: Dillalai sun yi tagumi, jama'a ba sa zuwa sayen raguna

Farashin rakuma a kasuwar Kano

Game da farashin rakuma a kasuwan Kano, Alka ya ce farashin ya fara daga N150,000 zuwa N500,000.

"Mun fi sayar da rakuma da farashinsu ya kama daga N150,000 zuwa N270,000. Ina ganin mutane sun karkata zuwa ga rakuma ne don rakumin N200,000 ya fi shanun N400,000 yawan nama," in ji Alka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164