Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sunyi Nasarar Cafke Daya Cikin Yan Boko Haram Da Suka Tsere Daga Gidan Yarin Kuje

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sunyi Nasarar Cafke Daya Cikin Yan Boko Haram Da Suka Tsere Daga Gidan Yarin Kuje

  • Jaruman yan sanda a Jihar Nasarawa sunyi nasarar kama daya cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje a Abuja
  • An kama, wanda ake zargi dan Boko Haram ne, Hassan Hassan a karamar hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa yana kokarin tserewa
  • Mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatarwa manema labarai hakan a Lafia

Nasarawa - Biyo bayan harin da aka kai a gidan yarin Kuje da ke Abuja a baya-bayan nan tare da tserewar fursunoni, Rundunar yan sandan Nasarawa ta ce ta kama wani Hassan Hassan, wanda sunansa da hotonsa ke cikin fursunoni da aka ce sun tsere cikin wadanda ake zargin yan Boko Garam ne a karamar hukumar Keffi.

Kara karanta wannan

Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

Suspected BH Members.
Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Kama Daya Cikin Yan Boko Haram Da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje
Asali: Twitter

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Lafia, ranar Asabar, The Punch ta rahoto.

Suspected BH Member arrested
Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Kama Daya Cikin Yan Boko Haram Da Ya Tsere Daga Gidan Yarin Kuje. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce:

"Dakarun jami'an yan sandan ne suka kama wanda ake zargin dan Boko Haram ne da ya tsere a karamar hukumar Keffi na Jihar.
"Kwamishinan yan sanda, CP Adesina Soyemi, ya bada umurnin a kai wanda ake zargin wani wuri mai tsaro yayin da ake cigaba da neman sauran wadanda suka gudun domin mika su ga hukumar da ta dace.
"CP Soyemi ya gode wa jami'an yan sandan saboda jajircewa ya kuma bawa al'umma tabbacin rundunar za ta cigaba da kokarin samar da tsaro ga kowa."

Harin Gidan Yarin Kuje: Na Gargadi Aregbesola Kan Harin, Dakta Sadiq

A wani rahoton, Dakta Sadiq Amali na sashin nazarin halayar mutane a Jami'ar Tarayya ta Jigawa ya bayyana cewa ya yi hasashen za a kai hari gidan yarin Kuje a Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere

Yayin da ya ke magana kan harin a shirin Sunrise Daily na Channels TV, Dakta Amali ya ce ya rubuta wasika ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbsola, game da yiwuwar kai harin.

Yan bindiga da ake kyautata zaton yan ta'adda ne, daruruwansu sun kai hari gidan yarin a ranar Talata da dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164