Babban Sallah: Biyayya Ga Koyarwar Addini Zai Magance Mafi Yawancin Matsalolin Mu, Buhari

Babban Sallah: Biyayya Ga Koyarwar Addini Zai Magance Mafi Yawancin Matsalolin Mu, Buhari

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce idan da yan Najeriya na biyayya da koyarwar addinai, da tuni mafi yawancin matsalolin da ke adabar kasar sun gushe
  • Cikin sakonsa na babban sallah, Buhari ya bada misalin yadda rashin biyayya da koyarwar addini ke saka yan kasuwa tsawalla farashi da masu rike da mukami satar kudin talakawa
  • Buharin, bayan taya musulmin Najeriya da duniya murna ya bukaci a yi amfani da bikin don yin addu'o'i ga kasa da nuna kauna ga juna da sadaukarwa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce idan yan Najeriya za su rika aiki da koyarwar addinai, da an warware mafi yawancin matsalolin da ke adabar al'umma, Nigerian Tribune ta rahoto.

A sakonsa na babban sallar ga musulmin kasar da sauran mutane a ranar Juma'a, Shugaba Buhari ya yi kira da al'umma su fifita kasa kan bukatun kansu kuma "su yi amfani da addini don zaburar da su son al'umma."

Kara karanta wannan

Hajj 2022: Yadda alhazan Najeriya da na duniya su ka yi cincirindo a Dutsen Arfah

Shugaba Muhammadu Buhari.
Babban Sallah: Biyayya Ga Koyarwar Addini Zai Magance Mafi Yawancin Matsalolin Mu, Buhari. Hoto: @nigeriantribune.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Idan muka yin ayyuka da koyarwa addini, mafi yawancin munanan abubuwan da suke adabar mu za su warware," in ji shi.

A cewar shugaban kasar, bai kamata a rika amfani da addini kawai a matsayin abin nunawa, amma a matsayin abin da zai zaburar da mutane don yin ayyukan alheri ga kasa da al'umma.

Ya yi bayanin cewa tsawalla farashi da yan kasuwa ke yi da satar kudaden al'umma da ma'aikatan gwamnati ke yi da sauran cin amana alama ne da ke nuna an yi watsi da koyarwar addinan mu.

"Al'ummar mu na cike da halaye masu sabani da juna. Mutane na nuna addini a fili amma babu tsoron Allah; suna kuntatawa wasu; kudi ya zama Ubangijinsu; shugabanni sun yi watsi da rantsuwar kama aiki suna daukan kudin al'umma suna karkatarwa zuwa aljihunsu," in ji shi.

Kara karanta wannan

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

Shugaba Buhari ya taya al'ummar musulmi a Najeriya da duniya murnar bikin sallah ya kuma ambaci jaruman maza da mata masu kayan damara da ke yaki da yan ta'adda da iyalansu da kuma wadanda ke tsare hannun azzaluman yan ta'adda.

Ya yi amfani da damar ya yi kira ga musulmi su yi amfani da sallar su yi nazari kan darrusan da ke cikin salla su kuma kaunaci juna su guji alaka da munanan akidoji da ke bawa shafawa musulunci bakin fenti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164