Hukumar Alhazai Na Kaduna Ta Tabbatar Da Rasuwar Daya Cikin Alhazanta A Ranar Arafat

Hukumar Alhazai Na Kaduna Ta Tabbatar Da Rasuwar Daya Cikin Alhazanta A Ranar Arafat

  • Hukumar jin dadin alhazai na Jihar Kaduna ta tabbatar da rasuwar Hajiya Asiya Aminu daga a kasa mai tsarki
  • Dr Usman Galadima, Shugaban sashin ayyuka kuma Jagoran likitocin Najeriya ya ce zuwa yanzu ba a tabbatar da sanadin rasuwarta ba
  • Hajiya Asiya ce maniyaciya ta biyu da ta rasu cikin alhazan Najeriya kawo yanzu a hajjin na shekarar 2022

Hukumar jin dadin alhazai na Jihar Kaduna ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazanta Hajiya Asiya Aminu daga karamar hukumar Zaria a yau Juma'a ranar a Arafat kuma a filin Arafat.

Sanarwar ta fito daga bakin Umar Shehu Zaria kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook a ranar Juma'a.

Hajiya Asiya Aminu
Hukumar Alhazai Na Kaduna Ta Tabbatar Da Rasuwar Daya Cikin Alhazanta A Ranar Arafat. Hoto: Umar Shehu Zaria.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

An Tiso Keyar Maniyattan Kano 7 Daga Saudiyya Zuwa Najeriya Saboda Biza Ta Bogi

Hakazalika, ita ma hukumar jin dadin alhazai na kasa NAHCON ta tabbatar da rasuwar na Hajiya Asiya Aminu, rahoton Nigerian Tribune.

Ta rasu ne yayin da ta ke barci jim kadan bayan dawowa daga Hawan Arafat a cewar makwabta da ke tanti.

Dr Usman Galadima, Shugaban sashin ayyuka kuma Jagoran likitocin Nigeria ya ce kawo yanzu ba a tabbatar da sanadin rasuwarta ba.

Ya ce an sanar da iyalanta kuma za a yi mata jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Asiya ita ce maniyyaciya ta biyu da ta rasu a kasa mai tsarki a hajjin 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi Jihar Nasarawa ta rasu a makon da ta gabata bayan gajeruwar rashin lafiya an kuma mata jana'iza a Makkah.

Tsayuwan Arafah na cikin farillun aikin hajji.

Maniyyatan Najeriya na cikin miliyoyi da suka yin aikin hajjin na 2022.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164