Harin gidan yarin Kuje: Buhari na ganawa da shugabannin tsaro
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga labule da shugabannin tsaro da manyan yan majalisarsa
- Ganawar wanda ke kan gudana a yanzu haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja ba ya rasa nasaba da fashin magarkamar Kuje da yan ta'adda suka yi
- A makon nan ne aka samu hargitsi yayin da wasu 'yan ta'adda da ake zaton yan Boko Haram ne suka farmaki gidan yarin na Kuje da daddare
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawa da shugabannin tsaro da ministoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja a safiyar ranar Juma’a, 8 ga watan Yuli.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa ganawar na da nasaba da farmakin da yan ta’adda suka kai gidan gyara hali na Kuje.
An tattaro cewa akalla fursunoni 600 ciki harda mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram ne suka tsere a yayin harin.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Farouk Yahaya, shugaban sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo da Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan majalisar shugaban kasa da suka halarci taron sun hada da ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, takwaransa na harkokin yan sanda, Mohammed Dingyadi.
Sai ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da ministan shari’a kuma Atoni Janar na tarayya, Abubakar Malami.
Fashin magarkamar Kuje: FG ta fitar da bayanan 'yan Boko Haram din da suka tsere
A gefe guda, mun ji cewa Hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya ta bayyana neman wasu kasurguman mutane 64 ruwa a jallo daga da suka tsere daga fashin magarkamar Kuje ta babban birnin tarayya Abuja.
Dangane da bayanin da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Umar ya fitar, wadanda suka tsere an ce ‘yan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ne.
Idan baku manta ba, an samu hargitsi yayin da wasu 'yan ta'adda suka farmka gidan yarin tare da sakin fursunoni daruruwa.
Asali: Legit.ng