Dirama yayin da Wani mutumi ya fara gudanar da aikin Hajji a sansanin Alhazai na Kano
- Wani mutumi ya ja hankalin mutane yayin da ya ayyana cewa tuni ya fara aikin Hajjinsa a sansanin Alhazai na jihar Kano
- Malam Jibrin Abdu daga garin Gezawa a jihar Kano ya ce zai dawo ya ƙarisa aikinsa tun da akwai dukkanin kayan aiki a wurin
- Wata Suwaiba Sani ta ce ba zata taba yafe wa duk mai hannu a rashin zuwanta sauke farali ba a bana 2022
Kano - Wani abu kamar wasan kwaikwayo ya faru a Kano ranar Alhamis yayin da wani maniyyaci da bai samu shiga rukunin ƙarshe da jirgi ya ɗiba zuwa ƙasa mai tsarki ba, ya ayyana cewa zai gudanar da Hajjinsa cikakke a sansanin Alhazai.
Malam Jibrin Abdu daga garin Gezawa ya zama abun kallo bayan an gan shi cikin shigar farin Harami kuma ya bayyana cewa tuni ya fara aikin Hajjinsa a sansanin.
Daily Trust ta ruwaito Mutumin ya ce:
"Na fara tun tuni tunda muna da kayan aiki baki ɗaya anan kuma tabbas zan dawo na ƙarisa aikin Hajji na cikakke. Na san yadda ake yi domin wannan ba shi ne karon farko ba kuma ba zai zama na karshe ba."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa ya siyar da Gonarsa domin ya samu damar zuwa sauke farali bana, "Amma wasu gurɓatattun jagorori suka hana mafarkinsa cika," duk da ya rungumi ƙaddara ya san haka Allah ya tsara.
Yadda Maniyyata suka nuna fushin su
Bayan Malam Abdu, wata mata mai suna Suwaiba Sani, tare da wasu da dama sun saki ruwan maganganu kan, "duk masu hannu a rashin tafiyar mu."
Matar wacce aka ji tana magana cikin fushi, ta jaddada cewa ba zata taɓa yafe wa duk wanda ya sa hannu a tafiyarta da sauran maniyyata zuwa Saudiyya ba ta yuwu ba, kamar yadda Punch ta rahoto.
Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa maniyyata 745 aka bari cirko-cirko a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano bayan Jirgin ƙarshe ya tashi da misalin ƙarfe 3:45 na yammacin Alhamis.
A wani labarin kuma An kama Jami'an tsaro biyu suna waya da yan ta'adda bayan harin gidan Yarin Kuje
Wata majiya ta bayyana cewa ana tsare da wasu yan sanda biyu bayan sun yi waya da yan ta'addan da suka tsere daga Gidan Yarin Kuje.
Bayanai sun nuna cewa yanzu haka ana cigaba da matsar yan sandan domin gano iya matakin haɗa kan da suka bayar.
Asali: Legit.ng