Hajji 2022: Maniyyata 1,000 sun yi cirko-cirko a sansanin Alhazai na jihar Kano

Hajji 2022: Maniyyata 1,000 sun yi cirko-cirko a sansanin Alhazai na jihar Kano

  • Maniyyatan jihar Kano 1,000 na na zaune suna jiran tsammani yayin da aka samu matsala da Azman Air
  • Shugaban hukumar jin daɗin Alhazai na Kano, Alhaji Ɗanbatta, ya ce maniyyatan na nan a sansani suna jira
  • Ya ce matsalar da aka samu tun farko shi ne na canjin kamfanin jirgin da zai jigilar daga Max Air zuwa Azman Air

Kano - Shugaban hukumar jin daɗin Alhazai na jihar Kano, Alhaji Mohammad Abba Dambatta, ya ce kamfanin jiragen sama na Azman Air ya kwashe maniyyata 1,386 zuwa ƙasa mai tsarki.

Rahoton Leadership ya tattara cewa maniyyata 1,000 na jihar Kano na nan a sansanin Alhazai suna jiran jirgin da zai zo ya kwashe su zuwa Saudiyya.

Ɗanbatta ya ce har yanzun akwai ragowar maniyyata 1,000 da ba su tashi zuwa ƙasa mai tsarki ba. Ya ƙara da cewa maniyyata 86 ba su samu Visar su ba har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: A karo na biyu, Saudiyya ta kara wa'adin jigilar Maniyyata zuwa kasa mai tsarki

Maniyyata na hawa jirgi.
Hajji 2022: Maniyyata 1,000 sun yi cirko-cirko a sansanin Alhazai na jihar Kano Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Shugaban hukumar ya ce yana da kwarin guiwa duk da cikas ɗin da kamfanin jiragen sama ke samu a wajen jigilar maniyyatan Kano zuwa ƙasa mai tsarki, ba bu wani maniyyaci da za'a bari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alhaji Ɗanbatta ya bayar da wannan tabbacin ne yayin zantawa da manema labarai a Ofishinsa ranar Laraba a jihar Kano, inda a cewarsa tabbas har yanzun mahajjana 1000 na nan zaune.

Meyasa aka samu matsala a hajjin bana?

Ya ce dalilin da ya sa hukumar ta samu matsaloli shi ne tun farko an yanke cewa jiragen Max Air ne zasu kwashe maniyyatan Kano, amma sai hukumar NAHCON ta soke da cewa, "Zamu yi aiki da jiragen Azman Air, wanda da farko muka yi fatali da hakan."

Ɗanbatta ya ce duk da sun bi hanyoyi don ganin an bar Max Air ya yi aikin, hukumar Alhazai ta ƙasa ta ƙeƙashe kasa ta ce Azman Air ne zai jigilar maniyyatan Kano.

Kara karanta wannan

A kowace rana mutanen jihata na cinye abincin Biliyan N4.5bn da nama mai yawa, Gwamna

Ya ce ya gaya wa gwamna Ganduje halin da ake ciki a lokacin kuma ya tashi takanas ta Kano ya je har Abuja domin ya roki NAHCON ta bar Max Air ya yi aiki a jiharsa amma aka watsa wa bukatarsa ƙasa a ido.

Shin Azman ya yi aikin da ya kamata?

Shugaban hukumar jin daɗin alhazan ya ƙara da bayanin cewa bayan hukumar ta tabbatar ba wata mafita dole Azman Air ne zai aikin jigilar mutanen, zuwa yanzu ya yi sawu biyar.

Punch ta rahoto Ya ce:

"Jirgin farko ya ɗauki mutum 399, na biyu ya kwashi maniyyata 97, a sawu na uku ya ɗibi mutum 95, yayin da jirgi na hudu ya kwashi 395 da kuma na ƙarshe da ya ɗibi Fasinjoji 100."

Wane Mataki Azman ke ɗauka na shawo kan matsalolin?

Yayin da jaridar da tuntuɓi kamfanin Azman Air domin jin ta bakin su, babban Manajan Kamfanin, Alhaji Suleiman Lawan, ya ce suna kan aikin shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka ɗora shi kan daddumar Sallah

Ya ce tuni suka sanar da NAHCON cewa ba zasu iya kwashe maniyyatan Kano ba baki ɗaya kuma ta yi alƙawarin samar da manyan jirage biyu da zasu taimaka a kwashe waɗan da suka rage.

A wani labarin kuma Mambobin ASUU 10 sun rasu saboda rashin biyan su Albashi a wannan Jami'ar ta jihar Edo

Malamai 10 na jami'ar Ambrose Alli University da ke jihar Edo sun rasa rayukan su saboda rashin biyan su Albashi na watanni 19.

Shugaban ASUU reshen jami'ar, Cyril Onogbosele, ya ce da yawan mambobin ba su iya siyan magungunan su, ga nauyin iyalai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262