Yajin Aiki: Mambobin ASUU 10 sun rasu saboda rashin biyan su Albashi a Jami'a ɗaya

Yajin Aiki: Mambobin ASUU 10 sun rasu saboda rashin biyan su Albashi a Jami'a ɗaya

  • Malamai 10 na jami'ar Ambrose Alli University da ke jihar Edo sun rasa rayukan su saboda rashin biyan su Albashi na watanni 19
  • Shugaban ASUU reshen jami'ar, Cyril Onogbosele, ya ce da yawan mambobin ba su iya siyan magungunan su, ga nauyin iyalai
  • Shugbaan ASUU na ƙasa, Farfesa Osodeeke, ya ziyarci jami'ar don nuna musu ana tare kan abubuwan da ke faruwa a Edo

Edo - Shugaban ƙungiyar Malaman Jami'o'i ASUU reshen jami'ar Ambrose Alli University, Cyril Onogbosele, ya ce sun rasa mambobin ƙungiyar guda 10 tun bayan shiga yajin aiki saboda rashin biyansu albashi.

Onogbosele ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya jagoranci wakilai zuwa jami'ar don nuna ana tare da zanga-zanga kan rashin biyansu Albashi da wasu matsaloli.

Ambrose Alli University.
Yajin Aiki: Mambobin ASUU 10 sun rasu saboda rashin biyan su Albashi a Jami'a ɗaya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito shugaban ASUU na jami'ar na cewa:

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Dukkan kasurguman 'yan Boko Haram da ke daure a Kuje sun tsere, inji minista

"Tun da aka fara yajin aikin, mun yi rashin Lakcarori 10, ma'aikata ba su samun Albashin su, wasu daga cikin su mun san su sosai, ba zasu iya cigaba da siyan magungunan rashin lafiyar su ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An hana ma'aikata Albashin su na tsawon watanni 19, Da yawan mu sun rasa rayukansu sakamakon haka. Ba zamu iya sauke nauyin iyalan mu da ya rataya a kan mu ba saboda rashin Albashi."
"Muna buƙatar a gyara jami'o'in gwamnati, muna son gyara walwalar malamai, sake gina jami'o'i da ba su damar cin gashin kan su, shawo kan rashin isasshen kasafi da biyan haƙƙoƙi, burin mu kenan a wannan yajin aikin."

Meyasa suka zaɓi yin zanga-zanga?

Mista Onogbosele ya ƙara da cewa sun shirya zanga-zangan ne domin jawo hankalin al'ummar jihar Edo su san abin da gwamna Godwin Obaseki, ya musu da kuma tilasta masa ya shawo kan matsalolin.

Kara karanta wannan

'Ba zata saɓu ba' Jam'iyyar APC ta tashi tsaye, ta fara shirin dakile sauya shekar wasu mambobinta zuwa PDP

Da yake nasa jawabin, shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Osodeke, ya ce uwar ƙungiyar ta ƙasa ta zo Ekpoma ne domin nuna ana tare da reshenta na jami'an kan matakin gwamna Obaseki na hana harkokin ƙungiyoyi.

A wani labarin na daban kuma Hadimin Sheikh Gumi ya bayyana ƙungiyar da ta kai hari gidan Yarin Kuje

Yan ta'addan Ƙungiyar Ansaru, waɗan da suka kai farmaki tare da sace Fasinjojin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga watan Maris, su suka sake kai kazamin hari gidan Yarin Kuje ranar Talata da daddare.

Mai taimaka wa shahararren malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, kan harkokin yaɗa labari, Malam Tukur Mamu, shi ne ya bayyana haka a Kaduna ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel