'Ba zamu taɓa mika wuya ga yan ta'adda ba, Fadar shugaban ƙasa ta kare Buhari

'Ba zamu taɓa mika wuya ga yan ta'adda ba, Fadar shugaban ƙasa ta kare Buhari

  • Fadar shugaban kasa ta kare shugaba Buhari bisa yanke tafiyar Senegal duk da jerin hare-haren da aka kai Katsina da Abuja
  • Mai taimakawa shugaban ta fannin yaɗa labarai, Femi Adeshina, ya ce bai kamata ko da wasa wani ya miƙa wuya ga yan ta'adda ba
  • A cewarsa da zaran irin waɗannan ayyukan sun fara hana shugaban gudanar ayyukansa, lallai kamata ya yi kowa ya miƙa wuya

Abuja - Hadimin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na musamman ta ɓangaren yada labarai, Femi Adesina, ya ce shugaban kasa zai fice daga Najeriya kamar yadda aka tsara.

A rahoton Daily Trust, Adeshina ya ce shugaban zai tafi ƙasar wajen duk da halin a ƙasa ke ciki saboda bai dace wani ya miƙa wuya ga ayyukan yan ta'adda ba.

Ya yi wannan furucin ne ranar Laraba yayin da yake martani ga rubdugun sukar da aka yi wa matakin shugaban na cigaba da shirin tafiya don halartar taron ƙungiyar IDA na nahiyar Afirka a Dakar, Senegal.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai wa Ayarin motocin shugaba Buhari hari a Katsina, sun jikkata mutane

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
'Ba zamu taɓa mika wuya ga yan ta'adda ba, Fadar shugaban ƙasa ta kare Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Da yake ƙarin haske kan dalilin Buhari na tafiya Senegal, Femi Adeshina ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Eh, shugaban ƙasa zai tafi kuma ya kamata saboda akwai taron ƙasa-da-ƙasa da aka shirya wa shugabannin ƙasashe, ya kamata ya kasance a wurin. Bai kamata a miƙa wuya ga ayyukan yan ta'adda ba."
"Duk lokacin da irin haka ta fara dakatar da kai daga gudanar da ayyuka, daga nan kawai sai mu ɗaga hannu mu mika wuya."
"Saboda haka ya kamata shugaban ƙasa ya cigaba da shirin tafiyarsa, nauyin ƙasa da ƙasa ne da ya rataya a kansa. Nagode."

Legit.ng Hausa ta gano cewa shugaban kasan zai bar Abuja duk da jerangiyar hare-haren da aka kai cikin awanni 24 da suka shuɗe a jihar Katsina da babban birnin tarayya Abuja.

Abinda ya faru a Abuja da Katsina

Kara karanta wannan

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya nesanta kansa da wani Hoto da aka ɗora shi kan daddumar Sallah

A jihar Katsina, tawgaar ayarin motocin shugaban ƙasa na kan hanyar su ta zuwa Daura, mahaifar Buhari, yayin da wasu miyagun yan bindiga suka musu kwantan ɓauna suna buɗe musu wuta a kusa da Dutsin-ma.

A wani harin na daban kuma duk a jihar Katsina, yan bindiga suka harbe mataimakin kwamishinan yan sanda har lahira.

Haka nan kuma, wasu yan bindiga da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun fasa gidan Yarin Kuje, da ke Abuja, inda suka kwance fursunoni ciki har da manyan kasurguman yan Boko Haram.

A wani labarin kuma Ana kokarin ɗinke baraka wata ta kunno kai, tsohon shugaban tsagin APC ya fice daga jam'iyyar

Tsohon shugaban tsagin jam'iyyar APC reshen jihar Ribas, Golden Chioma, ya yi murabus daga kasancewar mamba.

Chioma, tsohom ɗan majalisar dokokin jihar ya ce ba zai iya cigaba da zama jam'iyyar da bata san halacci ba, tana watsi da mutane bayan sun mata wahala.

Kara karanta wannan

Shiroro: Buhari ya sha alwashin ceto 'yan China da aka sace, ya hukunta 'yan ta'adda

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262