Da duminsa: An sake cafke 'yan gidan yari 100 da suka arce daga kurkukun Kuje
- Jami'an gidajen gyaran hali tare da taimakon sojoji, 'yan sanda da kungiyoyin 'yan sa kai sun sake cafko mutum 100 da suka tsere daga kurkukun Kuje
- Wata majiyar cikin gida ta jaddada cewa, har a halin yanzu jami'an tsaron suna cigaba da duba dajika domin sake cafko wadanda suka tseren
- Ministan tsaro, Manjo Janar Magashi mai ritaya ya sanar da yadda mutum 600 da suka hada da 'yan Boko Haram 64 suka gudu daga gidan yarin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
FCT, Abuja - Kusan 'yan gidan yari 100 ne da suka arce daga matsakaiciyar gidan gyaran hali ta Kuje dake babban birnin tarayya a Abuja aka sake kamawa, jaridar Punch ta ruwaito hakan.
Kamar yadda ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya sanar, 'yan ta'addan Boko haram ne suka kai farmki gidan yarin inda suka saki mutum 600 ciki har da 'yan Boko Haram 64 dake tsare.
Jarida Punch ta ruwaito cewa, an cafke mutum 300 daga cikin wadanda suka tsere kuma ana kokarin damko sauran a dawo da su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai, wata majiya daga gidan yarin ta sanar da cewa, an sake damke wasu mutum 100 daga cikin wadanda suka arce.
Yace, "Kamar yadda kuke gani da kanku, ababen hawa suna ta shige da fice daga gidan gyaran halin. jami'anmu tare da taimakon sojoji, 'yan sanda da 'yan sa kai suna ta duba dajika. Sun samu gagarumar nasara.
"Mun sake kama wasu dari, baya ga wadanda aka kama tun farko kuma aka dawo da su. Hakazalika, babu abinda ya faru da Abba Kyari kamar yadda ake yadawa. Yana nan cikin gidan nan kuma lafiya kalau."
Harin gidan yarin Kuje: Fursunoni sama da 300 sun tsere
A wani labari na daban, Rahotanni sun kawo cewa fursunoni sama da guda 300 ne suka tsere daga babban gidan gyara hali na Kuje da ke babbar birnin tarayya Abuja.
Hakan ya biyo bayan farmakin da wasu mutane da ba a san ko su wanene ba suka kai gidan gyara halin a daren ranar Talata, 5 ga watan Yuli.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wata majiya ta gidan yari da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewar fiye da fursunoni 300 ne suka tsere a yayin harin yan bindigar.
Asali: Legit.ng